1
Fit 23:25-26
Littafi Mai Tsarki
HAU
Za ku bauta wa Ubangiji Allahnku, ni kuwa zan yalwata abincinku da ruwan shanku, in kuma kawar muku da ciwo. A ƙasarku, mace ba za ta yi ɓari ba, ba kuma za a sami marar haihuwa ba. Zan ba ku tsawon rai.
So sánh
Khám phá Fit 23:25-26
2
Fit 23:20
“Ni da kaina zan aiki mala'ika a gabanku don ya kiyaye ku a sa'ad da kuke tafiya, ya kuma kai ku inda na shirya muku.
Khám phá Fit 23:20
3
Fit 23:22
Idan kun kasa kunne a hankali ga maganarsa, kuka aikata dukan abin da na faɗa, sai in zama maƙiyin maƙiyanku da magabcin magabtanku.
Khám phá Fit 23:22
4
Fit 23:2-3
Kada ku yi mugunta domin galibin mutane na yi, kada kuwa ku yi shaidar zur a gaban shari'a don ku faranta zuciyar yawancin mutane, domin kada ku sa a kauce wa adalci. Kada ku yi wa matalauci sonkai a gaban shari'a.
Khám phá Fit 23:2-3
5
Fit 23:1
Kada ku baza rahoton ƙarya. Kada wani ya haɗa baki da mugu ya zama munafukin mashaidi.
Khám phá Fit 23:1