YouVersion Logo
Search Icon

Zab 98

98
Yabo saboda Adalcin Allah
1Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji,
Gama ya aikata ayyuka masu banmamaki!
Ta wurin ikonsa, da ƙarfinsa mai tsarki ya yi nasara.
2Ubangiji ya bayyana cin nasararsa,
Ya sanar da ikonsa na ceto ga sauran al'umma.
3Ya cika alkawarinsa wanda ya yi wa jama'ar Isra'ila,
Da tabbatacciyar ƙauna da aminci.
Dukan mutane ko'ina sun ga nasarar Allahnmu!
4Ku raira waƙa ta farin ciki ga Ubangiji.
Dukanku waɗanda suke a duniya,
Ku yabe shi da waƙoƙi, kuna ta da murya da ƙarfi,
Saboda farin ciki!
5Ku raira yabbai ga Ubangiji da garayu,
Ku kaɗa garayu!
6Ku busa kakaki da ƙahoni,
Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, Sarki!
7Ki yi ruri, ya ke teku,
Ke da dukan masu rai waɗanda suke cikinki,
Ki raira waƙa, ke duniya,
Da dukan waɗanda suke zaune cikinki!
8Ku yi tāfi, ya ku tekuna,
Ku raira waƙa tare, ya ku tuddai, don farin ciki.
9A gaban Ubangiji, gama ya zo ne ya yi mulki bisa duniya!
Zai yi mulki bisa dukan jama'ar duniya da adalci da gaskiya.

Currently Selected:

Zab 98: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in