YouVersion Logo
Search Icon

Zab 99

99
Amincin Allah ga Isra'ila
1 # Fit 25.22 Ubangiji Sarki ne,
Mutane suna rawar jiki,
Yana zaune a bisa kursiyinsa a bisa kerubobi,
Duniya ta girgiza.
2Ubangiji mai iko ne a Sihiyona,
Shi ne yake mulki a bisa dukan sauran al'umma.
3Kowa da kowa zai yabi sunansa mai girma, Maɗaukaki,
Mai Tsarki ne shi!
4Maɗaukaki kana ƙaunar abin da yake daidai,
Ka kawo adalci cikin Isra'ila,
Ka kawo adalci da gaskiya.
5Ku yabi Ubangiji Allahnmu,
Ku yi sujada a gaban kursiyinsa!
Mai Tsarki ne shi!
6Musa da Haruna firistocinsa ne,
Sama'ila kuma mai yi masa sujada ne.
Suka yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa musu.
7 # Fit 33.9 Ya yi magana da su daga girgije,
Suka yi biyayya da dokoki da umarnai da ya ba su.
8Ya Ubangiji Allahnmu, ka amsa wa jama'arka,
Ka nuna musu, kai Allah ne mai yin gafara,
Amma kakan hukunta su saboda zunubansu.
9Ku yabi Ubangiji Allahnmu,
Ku yi sujada a bisa dutsensa mai tsarki!
Ubangiji Allahnmu Mai Tsarki ne!

Currently Selected:

Zab 99: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in