YouVersion Logo
Search Icon

Zab 97

97
Allah Ne Mai Mulkin Dukka
1Ubangiji Sarki ne! Ki yi murna ke duniya!
Ku yi murna, dukanku tsibiran da suke cikin tekuna!
2Gajimare da duhu sun kewaye shi.
A kan adalci da gaskiya ya kafa mulkinsa.
3Wuta tana tafe a gabansa, tana cinye maƙiyansa
Waɗanda suke kewaye da shi.
4Walƙiyarsa ta haskaka duniya,
Duniya kuwa ta gani ta yi ta rawar jiki.
5Tuddai sun narke a gaban Ubangiji kamar kākin zuma,
A gaban Ubangijin dukan duniya.
6Sammai suna shelar adalcinsa,
Dukan kabilai kuwa, sun ga ɗaukakarsa.
7Dukan waɗanda suke yi wa siffofi sujada za su sha kunya,
Haka kuma waɗanda suke fāriya da gumakansu.
Dukan alloli za su rusuna a gabansa.
8Jama'ar Sihiyona suna murna,
Garuruwan Yahuza kuma suna farin ciki,
Sabili da irin shari'unka, ya Ubangiji!
9Ya Ubangiji Mai Iko Dukka, kai kake mulkin dukan duniya,
Ka fi sauran alloli duka girma.
10Ubangiji yana ƙaunar masu ƙin mugunta.
Yakan kiyaye rayukan jama'arsa,
Yakan cece su daga ikon mugaye.
11Haske yakan haskaka adalai,
Haka kuma murna ta cika ga masu nagarta.
12Dukanku adalai ku yi murna,
Saboda abin da Ubangiji ya yi!
Ku tuna da abin da Mai Tsarki ya yi,
Ku yi masa godiya!

Currently Selected:

Zab 97: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in