Zab 96
96
Allah Maɗaukakin Sarki Ne
(1Tar 16.23-33)
1Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji!
Ku raira waƙa ga Ubangiji, ya duniya duka!
2Ku raira waƙa ga Ubangiji, ku yabe shi!
Kowace rana ku ba da labari mai daɗi cewa,
“Ya cece mu!”
3Ku yi shelar ɗaukakar Ubangiji ga sauran al'umma,
Ku yi shelar ayyukansa masu girma ga dukan kabilai.
4Ubangiji da girma yake, tilas a ɗaukaka shi,
Tilas a fi jin tsoronsa fiye da dukan alloli.
5Allolin dukan al'ummai, gumaka ne kawai,
Amma Ubangiji ne ya yi sammai.
6Daraja da ɗaukaka suna kewaye da shi,
Girma da jamali suna cikin Haikalinsa.
7 #
Zab 29.1,2 Dukan jama'ar da suke bisa duniya su yabi Ubangiji!
Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa!
8Ku yabi sunan Ubangiji mai ɗaukaka,
Ku kawo sadaka, ku shiga Haikalinsa.
9Ku durƙusa a gaban Mai Tsarki, sa'ad da ya bayyana,
Ku yi rawar jiki a gabansa, ku duniya duka!
10A faɗa wa dukan sauran al'umma, “Ubangiji Sarki ne!
Duniya ta kahu da ƙarfi a wurin zamanta,
Ba za a iya kaushe ta ba,
Shi zai shara'anta dukan jama'a da adalci.”
11Duniya da sararin sama, ku yi murna!
Ki yi ruri, ya ke teku da dukan masu rai da suke cikinki,
12Ku yi murna ya ku filaye da dukan abubuwan da suke cikinku!
Sa'an nan itatuwan da suke cikin kurama
Za su ta da murya saboda farin ciki
13A gaban Ubangiji, gama ya zo ne ya mallaki duniya.
Zai mallaki dukan jama'ar duniya
Da adalci da gaskiya.
Currently Selected:
Zab 96: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979