Zab 95
95
Waƙar Yabo da Sujada
1Ku zo mu yabi Ubangiji!
Mu raira waƙa domin farin ciki ga mai kiyaye mu,
Da Mai Cetonmu!
2Mu zo gabansa da godiya,
Mu raira waƙoƙin farin ciki na yabo!
3Gama Ubangiji Allah ne mai iko,
Shi yake mulki bisa sauran alloli duka.
4Yana mulki bisa dukan duniya,
Daga zurfafan kogwannin duwatsu zuwa tuddai mafiya tsayi.
5Yana mulki bisa tekun da ya yi,
Da kuma bisa ƙasar da ya siffata.
6Ku zo, mu durƙusa, mu yi masa sujada,
Mu durƙusa a gaban Ubangiji, Mahaliccinmu!
7 #
Ibr 3.7-11
#
Ibr 3.15; 4.7 Shi ne Allahnmu,
Mu ne jama'ar da yake lura da ita,
Mu ne kuma garken da yake ciyarwa.
Yau ku ji abin da yake faɗa.
8 #
Fit 17.1-7; L.Ƙid 20.2-13 “Kada ku taurare zuciyarku yadda kakanninku suka yi a Meriba,
Kamar yadda suka yi a jeji a Masaha, a wancan rana.
9A can suka gwada ni suka jarraba ni,
Ko da yake da idanunsu suka ga abin da na yi dominsu.
10A shekara arba'in ɗin nan,
Jama'ar nan ta zama abar ƙyama gare ni,
‘Su marasa biyayya ne,’ in ji ni,
‘Gama sun ƙi bin umarnaina!’
11 #
L.Ƙid 14.20-23; M.Sh 1.34-36; Ibr 4.3,5;
M.Sh 12.9,10 Sai na ji haushi, na yi musu alkawari mai nauyi.
Na ce, ‘Faufau ba za ku shiga ƙasar da zan ba ku hutawa a ciki ba.’ ”
Currently Selected:
Zab 95: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979