Zab 94
94
Addu'ar Neman Sakayya
1Ya Ubangiji, kai Allah ne wanda yake yin hukunci,
Ka bayyana fushinka!
2Kai ne mai yi wa dukan mutane shari'a,
Ka tashi, ka sāka wa masu girmankai
Abin da ya dace da su!
3Har yaushe mugaye za su yi ta murna?
Har yaushe ne, ya Ubangiji?
4Har yaushe za su yi shakiyanci,
Su yi ta ɗaga kai?
Har yaushe, ya Ubangiji?
5Suna ragargaza jama'arka, ya Ubangiji,
Suna zaluntar waɗanda suke naka.
6Suna karkashe gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu,
Da kuma baƙin da suke zaune a ƙasarmu.
7Suna cewa, “Ai, Ubangiji ba ya ganinmu,
Allah na Isra'ila ba ya lura da abin da yake faruwa!”
8Ya jama'ata, ƙaƙa kuka zama dakikai, wawaye haka?
Sai yaushe za ku koya?
9Allah ya yi mana kunnuwa, shi ba zai ji ba?
Allah ya yi mana idanu, shi ba zai gani ba?
10Shi ne yake shugabancin sauran al'umma, ba zai hukunta su ba?
Shi ne yake koya wa dukan mutane, shi ba shi da sani ne?
11 #
1Kor 3.20
Ubangiji ya san tunaninsu,
Ya san kuma hujjojinsu na rashin hankali.
12Ya Ubangiji, mai farin ciki ne mutumin da kake koya wa,
Mutumin da kake koya masa shari'arka.
13Don ka ba shi hutawa a kwanakin wahala,
Kafin a haƙa wa mugaye kabari.
14Ubangiji ba zai rabu da jama'arsa ba,
Ba zai rabu da waɗanda suke nasa ba.
15Adalci kuma zai sāke dawowa cikin majalisun alƙalai,
Dukan adalai kuwa za su yi na'am da shi.
16Wa zai tsaya mini gāba da mugaye?
Wa zai goyi bayana gāba da masu aikata mugunta?
17Da ba domin Ubangiji ya taimake ni ba,
Ai, da tuni na kai ƙasar da ba a motsi.
18Na ce, “Ina kan fāɗuwa,”
Amma, ya Ubangiji, madawwamiyar ƙaunarka ta riƙe ni.
19Sa'ad da nake alhini, ina cikin damuwa,
Ka ta'azantar da ni, ka sa in yi murna.
20Ba ruwanka da alƙalai azzalumai, marasa gaskiya,
Waɗanda suka mai da rashin gaskiya ita ce gaskiyarsu,
21Sukan shirya wa mutanen kirki maƙarƙashiya,
Sukan yanke wa marar laifi hukuncin kisa.
22Amma Ubangiji yakan kāre ni,
Allahna yakan kiyaye ni.
23Shi zai hukunta su saboda muguntarsu,
Ya hallaka su saboda zunubansu.
Ubangiji Allahnmu zai hallaka su.
Currently Selected:
Zab 94: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979