Bible App logo
Search Icon

Zab 70

70
Addu'ar Neman Kuɓuta
1Ka cece ni, ya Allah!
Ya Ubangiji, ka yi hanzari ka taimake ni!
2Ka sa masu so su kashe ni,
A ci nasara a kansu, su ruɗe!
Ka sa waɗanda suke murna saboda wahalaina, su koma baya, su sha kunya!
3Ka sa waɗanda suke mini ba'a
Su razana sabili da fāɗuwarsu!
4Ka sa dukan waɗanda suke zuwa gare ka
Su yi murna, su yi farin ciki!
Ka sa waɗanda suke ƙaunar cetonka
Kullayaumi su ce, “Allah da girma yake!”
5Ba ni da ƙarfi, ba mataimaki,
Ya Allah, ka zo wurina da hanzari.
Kai ne mataimakina da Mai Cetona,
Kada ka yi jinkiri, ya Ubangiji!

Currently Selected:

Zab 70: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in