Bible App logo
Search Icon

Zab 71

71
Addu'ar Tsoho
1A gare ka, ya Ubangiji, lafiya lau nake,
Faufau kada ka bari a yi nasara da ni!
2Sabili da kai adali ne ka taimake ni, ka cece ni.
Ka kasa kunne gare ni, ka cece ni!
3Ka zama mini lafiyayyiyar mafaka,
Da kagara mai ƙarfi, domin ka tsare ni,
Kai ne mafakata da kāriyata.
4Ya Allahna, ka cece ni daga mugaye,
Daga ikon mugga, wato mugayen mutane.
5Ya Ubangiji, a gare ka nake sa zuciya,
Tun ina yaro, nake dogara gare ka.
6A duk kwanakina a gare ka nake dogara,
Kana kiyaye ni tun da aka haife ni,
Kullayaumi zan yabe ka!
7Raina abin damuwa ne ga mutane da yawa,
Amma kai ne kāriyata mai ƙarfi.
8Ina yabonka dukan yini,
Ina shelar darajarka.
9Yanzu da na tsufa, kada ka yashe ni,
Yanzu da ƙarfina ya ƙare kuma, kada ka rabu da ni!
10Maƙiyana, waɗanda suke so su kashe ni,
Suna magana, suna ƙulle-ƙulle gāba da ni.
11Suna cewa, “Ai, Allah ya rabu da shi,
Gama ba wanda zai cece shi!”
12Kada ka yi nisa da ni haka, ya Allah,
Ka yi hanzari ka taimake ni, ya Allahna!
13Ka sa a kori waɗanda suka tasar mini,
A hallaka su!
Ka sa a kunyata waɗanda suke ƙoƙari su cuce ni,
A wulakanta su sarai!
14A koyaushe zan sa zuciya gare ka,
Zan yi ta yabonka.
15Zan ba da labarin adalcinka,
Zan yi magana a kan cetonka duk yini,
Ko da yake ya fi ƙarfin in san shi duka.
16Zan tafi in yi yabon ikonka, ya Ubangiji Allah,
Zan yi shelar adalcinka,
Naka, kai kaɗai.
17Kai ne ka koya mini, ya Allah, tun lokacin da nake yaro,
Har wa yau kuwa ina ba da labarin ayyukanka masu banmamaki.
18Yanzu da na tsufa, na kuma yi furfura,
Kada ka rabu da ni, ya Allah!
Ka kasance tare da ni sa'ad da nake shelar ikonka da ƙarfinka ga mutanen dukan zamanai masu zuwa.
19Adalcinka, ya Allah, ya kai har sammai.
Ka aikata manyan ayyuka,
Ba waninka!
20Ka aiko mini da wahala da azaba,
Amma za ka mayar mini da ƙarfina,
Za ka tashe ni daga kabari.
21Za ka girmama ni har abada,
Za ka sāke ta'azantar da ni.
22Hakika zan yabe ka da garaya,
Zan yabi amincinka, ya Allahna.
Da garayata zan yi maka waƙoƙi,
Ya Mai Tsarki na Isra'ila.
23Zan ta da muryar farin ciki
Sa'ad da nake raira maka waƙar yabbai,
Zan raira waƙa da zuciya ɗaya,
Gama dā ka fanshe ni.
24Zan yi magana a kan adalcinka dukan yini,
Saboda an yi nasara da waɗanda suke ƙoƙari su cuce ni, sun ruɗe.

Currently Selected:

Zab 71: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in