Bible App logo
Search Icon

Zab 67

67
Waƙar Miƙa Hadaya ta Godiya
1Ka yi mana jinƙai, ya Allah, ka sa mana albarka,
Ka dube mu da idon rahama,
2Domin dukan duniya ta san nufinka,
Dukan sauran al'umma kuma su san cetonka.
3Da ma dukan mutane su yabe ka, ya Allah,
Da ma dukan mutane su yabe ka!
4Da ma sauran al'umma su yi murna, su raira waƙa ta farin ciki,
Domin kana yi wa jama'a shari'a ta adalci,
Kana kuma bi da dukan sauran al'umma.
5Da ma dukan mutane su yabe ka, ya Allah,
Da ma dukan mutane su yabe ka!
6Ƙasa ta ba da amfaninta,
Allah, wanda yake Allahnmu ne, ya sa mana albarka.
7Allah ya sa mana albarka,
Da ma dukan jama'a ko'ina su girmama shi.

Currently Selected:

Zab 67: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in