Zab 66
66
Waƙar Yabo da Miƙa Hadaya ta Godiya
1Ku yabi Allah da babbar murya ta farin ciki,
Ya jama'a duka!
2Ku raira waƙar darajar sunansa,
Ku yabe shi da ɗaukaka!
3Ku faɗa wa Allah cewa, “Al'amuran da kake aikatawa
Suna da banmamaki ƙwarai!
Ikonka yana da girma ƙwarai,
Har maƙiyanka sukan durƙusa a gabanka don tsoro.
4Duk wanda yake a duniya, yana yi maka sujada,
Yana raira maka waƙar yabbai,
Yana raira yabbai ga sunanka.”
5Zo, ka ga abin da Allah ya yi,
Ayyukansa masu ban al'ajabi
Waɗanda ya aikata ga mutane.
6 #
Fit 14.21;
Josh 3.14-17
Ya sa teku ta zama busasshiyar ƙasa,
Kakanninmu suka haye kogi da ƙafa.
A can muka yi farin ciki saboda abin da ya yi.
7Har abada yana mulki ta wurin ƙarfinsa,
Yana duban al'ummai,
Don kada 'yan tawaye su tayar masa!
8Ku yabi Allahnmu, ya ku dukan al'ummai,
Bari a ji yabon da kuke yi masa.
9Shi ne yake rayar da mu,
Bai kuwa yarda mu fāɗi ba.
10Ka jarraba mu, ya Allah,
Kamar yadda ake tace azurfa da wuta,
Haka nan ka jarraba mu.
11Ka bar mu muka fāɗa a tarko,
Ka ɗora mana kaya masu nauyi.
12Ka bar maƙiyanmu suka tattaka mu,
Mun ratsa ta cikin wuta da rigyawa,
Amma yanzu ka kawo mu a lafiyayyen wuri.
13Zan kawo hadayun ƙonawa a ɗakinka,
Zan miƙa maka abin da na alkawarta.
14Zan ba ka abin da na ce zan bayar,
A lokacin da nake shan wahala.
15Zan miƙa tumaki don a ƙona a kan bagade,
Nan za a ji ƙanshi mai daɗi na ƙonannun awaki,
Zan miƙa hadayu na bijimai da na awaki.
16Ku zo ku ji, dukanku, ku da kuke girmama Allah,
Ni kuwa zan faɗa muku abin da ya yi mini.
17Na yi kira gare shi neman taimako,
A shirye nake in yabe shi da waƙoƙi.
18Da ban watsar da zunubaina ba,
Da Ubangiji bai ji ni ba.
19Amma hakika Allah ya ji ni,
Ya saurari addu'ata.
20Ina yabon Allah,
Domin bai ƙi addu'ata ba,
Bai kuwa hana mini madawwamiyar ƙaunarsa ba.
Currently Selected:
Zab 66: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979