Zab 68
68
Waƙar Nasara ta Al'ummar Ƙasar
1Da ma Allah ya tashi ya warwatsa maƙiyansa!
Da ma su waɗanda suke ƙinsa su gudu!
2Kamar yadda iska take korar hayaƙi,
Haka nan zai kore su,
Kamar yadda kākin zuma yakan narke a gaban wuta,
Haka nan mugaye za su hallaka a gaban Allah.
3Amma adalai za su yi murna,
Su kuma yi farin ciki a gaban Allah,
Za su yi murna ƙwarai da gaske.
4Ku raira waƙa ga Allah,
Ku raira waƙar yabo ga sunansa,
Ku yi hanya ga wanda yake ratsa gizagizai.
Sunansa kuwa Ubangiji ne, ku yi murna a gabansa!
5Allah, wanda yake zaune a tsattsarkan Haikalinsa,
Yana lura da marayu, yana kuwa kiyaye gwauraye,
Wato matan da mazansu suka mutu.
6Yakan ba waɗanda suke da kewa gida, su zauna a ciki,
Yakan fitar da 'yan sarƙa ya kai su 'yanci mai daɗi,
Amma 'yan tawaye za su zauna a ƙasar da ba kowa a ciki.
7Sa'ad da ka bi da jama'arka, ya Allah,
Sa'ad da ka yi tafiya a hamada,
8 #
Fit 19.18
Duniya ta girgiza, sararin sama ya kwararo ruwa,
Saboda bayyanar Allah, har Dutsen Sinai ya girgiza,
Saboda bayyanar Allah na Isra'ila.
9Ka sa aka yi ruwan sama mai yawa, ya Allah,
Ka rayar da ƙasarka wadda ta zozaye.
10Jama'arka suka gina gidajensu a can,
Ta wurin alherinka ka yi wa matalauta tanadi.
11Ubangiji ya ba da umarni,
Sai mata masu yawa suka baza labari cewa,
12“Sarakuna da rundunan sojojinsu suna gudu!
Matan da suke a gida suka rarraba ganima.”
13Suna kamar kurciyoyin da aka dalaye da azurfa,
Waɗanda fikafikansu suna ƙyalli kamar kyakkyawar zinariya.
(Me ya sa waɗansunku suke zaune cikin shingen tumaki?)
14Sa'ad da Allah Mai Iko Dukka
Ya warwatsar da sarakuna a dutsen Zalmon,
Sai ya sa dusar ƙanƙara ta sauka a wurin.
15Wane irin babban dutse ne wannan dutsen Bashan?
Tulluwarka nawa, dutsen Bashan?
16Me ya sa, daga manyan kawunanka
Kake yi wa dutsen da Allah ya zaɓa
Ya zauna a kai, duban raini?
A nan Ubangiji zai zauna har abada!
17Daga Sinai da dubban manyan karusansa,
Ubangiji ya zo tsattsarkan Haikalinsa.
18 #
Afi 4.8
Ya hau kan tsaunuka
Tare da ɗumbun waɗanda ya kamo daga yaƙi,
Yana karɓar kyautai daga wurin mutane,
Daga wurin 'yan tawaye kuma.
Ubangiji Allah zai zauna a can.
19Ku yabi Ubangiji,
Wanda yake ɗaukar nawayarmu ta yau da kullum,
Shi ne Allah wanda ya cece mu.
20Allahnmu, Allah Mai Ceto ne,
Shi ne Ubangiji, Ubangijinmu,
Wanda yake cetonmu daga mutuwa.
21Hakika Allah zai farfashe kawunan abokan gābansa,
Da na waɗanda suka nace bin hanyoyinsu na zunubi.
22Ubangiji ya ce, “Zan komo da su daga Bashan,
Zan komo da su daga zurfin teku,
23Don ku wanke sawayenku a cikin jinin maƙiyanku,
Karnukanku kuwa za su lashe iyakar abin da suke so.”
24Ya Allah, jama'a duka sun ga irin tafiyarka ta nasara,
Irin tafiyar Allah, Sarkina, zuwa tsattsarkan wurinsa.
25Mawaƙa suna kan gaba, mabusa suna biye,
A tsakiya kuwa 'yan mata suna kaɗa bandiri.
26“Ku jama'ar Allah, ku yabe shi cikin taronku,
Ku yabi Ubangiji, dukanku, ku zuriyar Isra'ila!”
27Ga Biliyaminu mafi ƙanƙanta
Cikin kabilai, a kan gaba,
Sa'an nan shugabannin Yahuza da ƙungiyarsu,
Daga nan sai shugabannin Zabaluna da na Naftali suna biye da su.
28Ka nuna ikonka, ya Allah,
Ikon nan da ka nuna saboda mu.
29Daga Haikalinka a Urushalima,
Sarakuna sukan kawo maka kyautai.
30Ka tsauta wa Masar, naman jejin nan
Mai zafin hali da yake cikin iwa,
Ka tsauta wa sauran al'umma, taron bijiman nan da 'yan maruƙansu,
Har dukansu su durƙusa, su miƙa maka azurfarsu.
Ka warwatsar da jama'ar nan
Masu son yin yaƙi!
31Wakilai za su zo daga Masar,
Habashawa za su miƙa hannuwansu sama,
Su yi addu'a ga Allah.
32Ku raira waƙa ga Allah, ku mulkokin duniya,
Ku raira waƙar yabo ga Ubangiji,
33Shi wanda ya hau cikin sararin sama,
Daɗaɗɗen sararin sama!
Ku kasa kunne ga muryarsa mai ƙarfi!
34Ku yi shelar ikon Allah,
Ɗaukakarsa tana bisa kan Isra'ila,
Ikonsa yana cikin sararin sama.
35Allah al'ajabi ne a tsattsarkan wurinsa,
Allah na Isra'ila!
Yana ba da ƙarfi da iko ga jama'arsa.
Ku yabi Allah!
Currently Selected:
Zab 68: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979