Zab 58
58
Addu'a domin A Hukunta Mugaye
1Hakika za ku yanka daidai, ku manya?
Za ku shara'anta wa mutane daidai?
2A'a, tunanin muguntar da za ku aikata kaɗai kuke yi,
Kuna aikata laifofin ta da hargitsi a ƙasar.
3Mugaye, laifi suke yi dukan kwanakinsu,
Tun daga ranar da aka haife su suke ta faɗar ƙarya.
4Cike suke da dafi kamar macizai,
Sukan toshe kunnuwansu kamar kuraman gamsheƙa,
5Wanda ba ya jin muryar gardi,
Ko kuma waƙar gwanin sihiri.
6Ka kakkarya haƙoransu, ya Allah,
Ka ciccire fiƙoƙin waɗannan zakoki masu zafin rai, ya Ubangiji!
7Bari su ɓace kamar ruwan da ya tsanye,
Bari a murtsuke su kamar ciyayi a hanya.
8Bari su zama kamar katantanwu waɗanda sukan narke su yi yauƙi,
Allah ya sa su zama kamar jinjirin da aka haifa matacce.
Wanda bai taɓa ganin hasken rana ba.
9Kafin tukunya ta ji zafin wuta,
Da zafin fushi, Allah zai watsar da su tun suna da rai.
10Adalai za su yi murna sa'ad da suka ga an hukunta masu zunubi,
Za su wanke ƙafafunsu cikin jinin mugaye.
11Mutane za su ce, “Hakika an sāka wa adalai,
Hakika akwai Allah wanda yake shara'anta duniya!”
Currently Selected:
Zab 58: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979