Bible App logo
Search Icon

Zab 57

57
Addu'ar Neman Kuɓuta daga Tsanani
(Zab 108.1-5)
1Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi jinƙai,
Gama na zo gare ka neman tsira.
Zan sami kāriya a ƙarƙashin fikafikanka,
Sai dukan hatsari ya wuce.
2Zan yi kira ga Allah, Maɗaukaki,
Zan yi kira ga Allah, mai biyan dukan bukatata.
3Daga sammai Allah zai amsa mini,
Zai kori waɗanda suka tasar mini,
Allah zai nuna mini madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa.
4Raina yana tsakiyar zakoki,
Na kwanta a tsakiyar waɗanda suka yi niyyar cinye mutane.
Haƙoransu kamar māsu da kibau suke,
Harsunansu masu kaifi ne kamar takobi.
5Ka bayyana girmanka ya Allah, a sararin sama,
Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!
6Maƙiyana sun kafa tarko don su kama ni,
Damuwa ta fi ƙarfina.
Sun yi wushefe a kan hanyata,
Amma su da kansu suka fāɗa a ciki.
7A shirye nake, ya Allah,
Na shirya sosai!
Zan raira waƙoƙi in yabe ka!
8Ka farka, ya raina!
Ku farka, molona da garayata!
Zan sa rana ta farka!
9Zan gode maka a cikin sauran al'umma, ya Ubangiji!
Zan yabe ka a cikin jama'a!
10Madawwamiyar ƙaunarka ta kai har sammai,
Amincinka kuma har sararin sammai.
11Ka bayyana girmanka, ya Allah, a sararin sama,
Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!

Currently Selected:

Zab 57: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in