Zab 59
59
Addu'ar Neman Ceto daga Maƙiya
1Ka cece ni daga maƙiyana, ya Allahna,
Ka kiyaye ni daga waɗanda suka tasar mini!
2Ka cece ni daga waɗannan mugaye,
Ka tsirar da ni daga masu kisankan nan!
3Duba! Suna jira su auka mini,
Mugaye suna taruwa gāba da ni,
Ba domin wani zunubi ko wani laifin da na yi ba,
4Ba domin na yi wani laifi ba, ya Ubangiji,
Har da suka gaggauta gāba da ni.
Kai da kanka ka gani, ya Allah na Isra'ila!
Ka tashi ka taimake ni.
5Ka tashi, ya Ubangiji, Allah Maɗaukaki, ka taimake ni,
Ka tashi ka hukunta al'ummai,
Kada ka yi wa waɗannan mugaye, maciya amana, jinƙai!
6Da maraice suka komo,
Suna yaƙe haƙora kamar karnukan da suke yawo ko'ina a birni.
7Ji abin da suke fada!
Harsunansu suna kama da takuba a bakinsu,
Duk da haka suna ta tambaya, suna cewa, “Wa zai ji mu?”
8Amma kai dariya kake yi musu, ya Ubangiji,
Ka mai da al'ummai duka abin bandariya!
9Mai tsarona, kai ne kake kiyaye ni,
Kai ne mafakata, ya Allah.
10Allahna wanda yake ƙaunata, zai zo gare ni,
Zai sa in ga an kori magabtana.
11Kada ka kashe su, ya Allah, don kada jama'ata su manta.
Ka watsar da su da ikonka, ka hallaka su ya Ubangiji mai kiyaye mu!
12Zunubi na cikin leɓunansu, maganganunsu na zunubi ne,
Da ma a kama su saboda girmankansu,
Domin suna la'antarwa, suna ƙarya!
13Da fushinka ka hallaka su,
Ka hallaka su ɗungum.
Sa'an nan jama'a za su sani Allah yana mulkin Isra'ila,
Mulkinsa ya kai ko'ina a duniya!
14Da maraice maƙiyana suka komo,
Suna yaƙe haƙora kamar karnukan da suke yawo ko'ina a birni.
15Suna kai da kawowa ko'ina neman abinci,
In ba su sami abin da ya ishe su ba,
Sukan yi gunaguni.
16Amma zan raira waƙa a kan ikonka,
Kowace safiya zan raira waƙa da ƙarfi
Ga zancen madawwamiyar ƙaunarka.
Kai mafaka ne a gare ni,
Wurin ɓuya a kwanakin wahala.
17Zan yabe ka, mai tsarona,
Allah ne mafakata,
Allah wanda ya ƙaunace ni.
Currently Selected:
Zab 59: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979