Bible App logo
Search Icon

Zab 56

56
Addu'ar Dogara ga Allah
1Ka yi mini jinƙai, ya Allah,
Gama mutane sun tasar mini,
Maƙiyana suna tsananta mini koyaushe!
2Dukan yini maƙiyana suna tasar mini,
Waɗanda suke faɗa da ni sun cika yawa.
3Sa'ad da nake jin tsoro, ya Maɗaukaki,
A gare ka nake dogara.
4Ga Allah nake dogara, ina yabon alkawarinsa,
Gare shi na dogara, ba zan ji tsoro ba.
Me mutum kawai zai yi mini?
5Maƙiyana suke ta wahalshe ni dukan yini,
A kan kowane abu da nake yi,
Kullum suna ta tunanin yadda za su cuce ni!
6Sukan taru a ɓoye,
Suna kallon duk abin da nake yi.
Suna sa zuciya za su iya kashe ni.
7Ka hukunta su, ya Allah saboda muguntarsu,
Da fushinka ka kori waɗannan mutane!
8Ka san irin wahalar da nake sha,
Kana riƙe da lissafin yawan hawayena.
Ashe, ba a rubuce suke a littafinka ba?
9A ranar da na yi kira gare ka,
Za a komar da abokan gābana baya,
Gama na sani Allah yana tare da ni!
10Ina dogara ga Allah, ina yabon alkawarinsa,
Ina dogara ga Ubangiji, ina yabon alkawarinsa.
11A gare shi nake dogara,
Ba zan ji tsoro ba.
Me mutum kawai zai yi mini?
12Zan miƙa maka abin da na yi alkawari, ya Allah,
Zan miƙa maka hadaya ta godiya.
13Domin ka cece ni daga mutuwa,
Ka hana a ci nasara a kaina.
Saboda haka a gaban Allah nake tafiya
A hasken da yake haskaka wa masu rai.

Currently Selected:

Zab 56: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in