Zab 55
55
Addu'ar Neman Taimako
1Ka ji addu'ata, ya Allah,
Kada ka ƙi jin roƙona!
2Ka saurare ni, ka amsa mini,
Gama damuwata ta gajiyar da ni tiƙis.
3Hankalina ya tashi saboda yawan kurarin maƙiyana,
Saboda danniyar mugaye.
Sukan jawo mini wahala,
Suna jin haushina suna ƙina.
4Azaba ta cika zuciyata,
Tsorace-tsoracen mutuwa sun yi mini nauyi.
5Tsoro da rawar jiki sun kama ni,
Na cika da razana.
6Na ce, “Da a ce ina da fikafikai kamar kurciya,
Da sai in tashi, in tafi, in nemi wurin hutawa!
7In tafi can nesa,
In yi wurin zamana a hamada.
8Zan hanzarta in nemi mafaka
Daga iska mai ƙarfi da hadiri.”
9Ka hallaka su, ya Ubangiji, ka birkitar da maganarsu,
Gama na ga hargitsi da tawaye a birni.
10Dare da rana suna ta yawo a kan garu suna ta kewaye birnin,
Birnin kuwa cike yake da laifi da wahala.
11Akwai hallaka a ko'ina,
Tituna suna cike da azzalumai da 'yan danfara.
12Da a ce maƙiyina ne yake mini ba'a,
Da sai in jure.
Da a ce abokin gābana ne yake shugabancina,
Da sai in ɓuya masa.
13Amma kai ne, aminina,
Abokin aikina ne, abokina ne kuma!
14Dā mukan yi taɗi da juna ƙwarai,
Mukan tafi Haikali tare da sauran jama'a.
15Allah ya sa mutuwa ta auko wa maƙiyana ba labari,
Allah ya sa su gangara ƙasar matattu da ransu!
Mugunta tana cikin gidajensu da zukatansu.
16Amma ina kira ga Allah, yă taimake ni,
Ubangiji kuwa zai cece ni.
17Koke-kokena da nishe-nishena
Suna hawa zuwa gare shi da safe, da tsakar rana, da dad dare,
Zai kuwa ji muryata.
18Zai fisshe ni lafiya
Daga yaƙe-yaken da nakan yi da magabtana masu yawa.
19Allah, shi wanda yake mulki tun fil azal,
Zai ji ni, zai kore su.
Ba abin da suka iya yi a kai,
Domin ba su tsoron Allah.
20Abokina na dā,
Ya yi wa abokansa faɗa,
Ya ta da alkawarinsa.
21Kalmominsa sun fi mai taushi,
Amma ƙiyayya tana a zuciyarsa,
Kalmominsa sun fi mai sulɓi,
Amma suna yanka kamar kakkaifan takobi.
22Ka gabatar da wahalarka ga Ubangiji,
Zai kuwa taimake ka,
Ba zai bari a ci nasara a kan mutumin kirki ba, faufau.
23Amma kai, ya Allah, za ka jefar da masu kisankai, da maƙaryata can ƙasa cikin zurfafa,
Kafin su kai rabin kwanakinsu a duniya.
Amma ni, zan dogara gare ka.
Currently Selected:
Zab 55: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979