Zab 54
54
Addu'ar Neman Tsari daga Maƙiyi
1Ka cece ni ta wurin ikonka, ya Allah,
Ka cece ni ta wurin ƙarfinka!
2Ka ji addu'ata, ya Allah,
Ka saurari kalmomina!
3Masu girmankai sun tasar mini,
Mugaye suna nema su kashe ni,
Mutanen da ba su kula da Allah ba.
4Na sani Allah ne mai taimakona,
Na sani Ubangiji shi ne mai tsarona!
5Ubangiji ya hukunta wa maƙiyana da irin muguntarsu!
Gama zai hallaka su saboda shi mai aminci ne.
6Da murna zan miƙa maka hadaya,
Zan yi maka godiya, ya Ubangiji,
Domin kai mai alheri ne.
7Ka cece ni daga dukan wahalaina,
Na kuwa ga an kori maƙiyana.
Currently Selected:
Zab 54: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979