Zab 50
50
Allah ne Mai Shari'a
1Allah Maɗaukaki, Ubangiji, ya yi magana,
Yana kiran dukan duniya, daga gabas zuwa yamma.
2Allah yana haskakawa daga Sihiyona,
Da cikar jamalin Sihiyona.
3Allahnmu ya zo, ba a ɓoye yake ba,
Wuta mai cinyewa na tafe a gabansa,
Babban hadiri kuwa na kewaye da shi.
4Ya kira sammai da duniya su zama shaidu,
Su ga yadda yake shara'anta jama'arsa.
5Ya ce, “Ku tattaro mini amintattuna,
Waɗanda suka cika alkawarin da yake tsakanina da su,
Ta wurin miƙa hadaya.”
6Sammai suna shelar adalcin Allah,
Domin shi yake yin shari'a!
7“Ku ji, ya ku jama'ata, zan kuwa yi magana,
Zan ba da shaida gāba da ku, ya Isra'ila.
Ni ne Allah, Allahnku.
8Ban tsauta muku saboda hadayunku ba,
Ko saboda hadayu na ƙonawa da kuke ta miƙa mini kullum.
9Ba na bukatar bijimai daga gonakinku,
Ko awaki daga garkunanku.
10Gama namomin jeji nawa ne,
Dubban shanu da suke kan tuddai kuma nawa ne.
11Dukan tsuntsayen da suke tashi a sararin sama nawa ne,
Da dukan masu rai da suke ƙasa.
12“Da ina jin yunwa ba sai na faɗa muku ba,
Gama da duniya da dukan abin da yake cikinta nawa ne.
13Nakan ci naman bijimai ne?
Ko nakan sha jinin awaki?
14Bari ku miƙa wa Allah hadayarku ta godiya,
Ku ba Mai Iko Dukka, dukan hadayun da kuka alkawarta.
15Ku yi kira gare ni sa'ad da wahala ta zo,
Zan cece ku,
Ku kuwa za ku yabe ni.”
16Amma Allah ya ce wa mugaye,
“Don me za ku haddace umarnaina?
Don me za ku yi magana a kan alkawaraina?
17Kun ƙi in tsauta muku,
Kun yi watsi da umarnaina.
18Sa'ad da kuka ga ɓarawo kukan yi abuta da shi.
Kuna haɗa kai da mazinata.
19“Kullum a shirye kuke ku hurta mugunta,
Ba ku jin nauyin faɗar ƙarya.
20A shirye kuke ku sari 'yan'uwanku,
Ku sa musu laifi.
21Kun aikata waɗannan duka, ni kuwa ban ce kome ba,
Saboda haka kuka zaci ni kamar ku nake.
Amma yanzu zan tsauta muku,
In bayyana muku al'amarin a fili.
22“Ku ji wannan ku da kuke ƙyale ni,
In ba haka ba zan hallaka ku,
Ba wanda zai cece ku.
23Wanda yake yin godiya a sa'ad da yake miƙa hadayarsa, yana girmama ni,
Da wanda yake yi mini biyayya kuma, zan nuna masa cetona.”
Currently Selected:
Zab 50: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979