Zab 51
51
Addu'ar Roƙon Gafara
1Ka yi mini jinƙai, ya Allah,
Sabili da madawwamiyar ƙaunarka.
Ka shafe zunubaina,
Saboda jinƙanka mai girma!
2Ka wanke muguntata sarai,
Ka tsarkake ni daga zunubina!
3Na gane laifina,
Kullum ina sane da zunubina.
4 #
Rom 3.4
Na yi maka zunubi, kai kaɗai na yi wa,
Na kuwa aikata mugunta a gare ka.
Daidai ne shari'ar da ka yi mini,
Daidai ne ka hukunta ni.
5Mugu ne ni tun lokacin da aka haife ni,
Mai zunubi ne ni tun daga ranar da aka haife ni.
6Amintacciyar zuciya ita kake so,
Ka cika tunanina da hikimarka.
7Ka kawar da zunubina, zan kuwa tsarkaka,
Ka wanke ni, zan kuwa fi auduga fari.
8Bari in ji sowa ta farin ciki da murna.
Ko da yake ka ragargaza ni,
Ka kakkarya ni, duk da haka zan sāke yin murna.
9Ka kawar da fuskarka daga zunubaina,
Ka shafe duk muguntata.
10Ka halitta tsarkakakkiyar zuciya a cikina, ya Allah,
Ka sa sabon halin biyayya a cikina.
11Kada ka kore ni daga gabanka,
Kada ka ɗauke mini Ruhunka Mai Tsarki.
12Ka sāke mayar mini da farin ciki na cetonka,
Ka ƙarfafa ni da zuciya ta biyayya.
13Sa'an nan zan koya wa masu zunubi umarnanka,
Za su kuwa komo wurinka.
14Ka rayar da raina, ya Allah Mai Cetona,
Zan kuwa yi shelar adalcinka da farin ciki.
15Ka taimake ni in yi magana, ya Ubangiji,
Zan kuwa yabe ka.
16Ba ka son sadakoki, ai, da na ba ka,
Ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa.
17Hadayata, ita ce halin ladabi, ya Allah,
Zuciya mai ladabi da biyayya,
Ba za ka ƙi ba, ya Allah.
18Ya Allah, ka yi wa Sihiyona alheri, ka taimake ta,
Ka sāke gina garun Urushalima.
19Sa'an nan za ka ji daɗin hadaya ta ainihi,
Da dukan hadayun ƙonawa.
Za a miƙa bijimai hadayu a bisa bagadenka.
Currently Selected:
Zab 51: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979