Zab 49
49
Dogara ga Dukiya Wauta Ce
1Ku ji wannan, ko wannenku,
Ku saurara jama'a duka na ko'ina,
2Da manya da ƙanana duka ɗaya,
Da attajirai da matalauta baki ɗaya.
3Zan yi magana da hikima,
Zan yi tunani mai ma'ana.
4Zan mai da hankalina ga ka-cici-ka-cici,
In bayyana ma'anarsa sa'ad da nake kaɗa molo.
5Don me zan ji tsoro a lokacin hatsari,
Sa'ad da mugaye suka kewaye ni,
6Mutanen da suke dogara ga dukiyarsu,
Waɗanda suke fariya saboda yawan wadatarsu?
7Har abada mutum ba zai iya fansar wani ba,
Ba kuwa zai iya biyan kuɗin ransa ga Allah ba.
8Gama kuɗin biyan ran mutum ba shi da iyaka.
Abin da zai iya biya, sam ba zai isa ba,
9Ba kuwa zai rayar da shi,
Ko ya hana shi mutuwa har abada ba.
10Yakan sa masu hikima su ma su mutu,
Haka nan ma wawaye da mutanen banza,
Za su mutu su bar dukiyarsu ga zuriyarsu.
11Kaburburansu za su zama gidajensu har abada,
Can za su kasance kullum,
Ko da yake a dā suna da ƙasa ta kansu.
12Girman mutum ba zai hana shi mutuwa ba,
Zai mutu kamar dabba.
13Dubi abin da zai faru ga waɗanda suke dogara ga kansu,
Da irin ƙaddarar waɗanda dukiya ta ishe su.
14Za a ƙaddara su ga mutuwa kamar tumaki,
Mutuwa ce za ta yi kiwonsu.
Da safe adalai za su ci nasara a kansu,
Sa'ad da gawawwakinsu suke ruɓewa a ƙasar matattu,
Nesa da gidajensu.
15Amma Allah zai fanshe ni,
Zai ɗauke ni daga ikon mutuwa.
16Kada ka damu sa'ad da mutum ya zama attajiri,
Ko kuwa dukiyarsa ta ƙasaita,
17Domin ba zai ɗauke ta a lokacin mutuwarsa ba,
Dukiyarsa ba za ta shiga kabari tare da shi ba.
18Ko da a ce mutum ya sami falalar wannan rai,
Ana kuwa ta yabonsa saboda nasarar da ya ci,
19Duk da haka zai tarar da kakanninsa waɗanda suka mutu,
Inda duhu ya dawwama har abada.
20Girman mutum ba zai hana shi mutuwa ba,
Zai mutu kamar dabba.
Currently Selected:
Zab 49: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979