YouVersion Logo
Search Icon

Zab 3

3
Addu'ar Safe ta Dogara ga Allah
1Ina da maƙiya da yawa, ya Ubangiji,
Da yawa kuma sun juya, suna gāba da ni!
2Suna magana a kaina, suna cewa,
“Allah ba zai taimake shi ba!”
3Amma kai, ya Ubangiji, kullum kana kiyaye ni daga hatsari,
Kana ba ni nasara,
Kana kuma maido mini da ƙarfin halina.
4Na yi kira wurin Ubangiji domin taimako,
Ya kuwa amsa mini daga tsattsarkan dutsensa.
5Na kwanta na yi barci,
Na kuwa tashi lafiya lau,
Gama Ubangiji yana kiyaye ni.
6Ba na jin tsoron dubban abokan gāba
Waɗanda suka kewaye ni ta kowane gefe.
7Ka zo, ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna!
Ka yi nasara a kan dukan abokan gābana,
Ka hallakar da dukan mugaye.
8Ceto yana zuwa daga wurin Ubangiji,
Bari yă sa wa jama'arsa albarka!

Currently Selected:

Zab 3: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy