YouVersion Logo
Search Icon

Zab 2

2
Mulkin Sarkin da Ubangiji Ya Zaɓa
1 # A.M 4.25,26 Don me al'ummai suke shirin tayarwa?
Don me waɗannan mutane suke ƙulla shawarwarin banza?
2Sarakunan duniya sun yi tayarwa,
Masu mulkinsu suna shirya maƙarƙashiya tare,
Gāba da Ubangiji da zaɓaɓɓen sarkinsa.
3Suna cewa, “Bari mu 'yantar da kanmu daga mulkinsu,
Bari mu fice daga ƙarƙashinsu!”
4Ubangiji ya yi dariya daga kan kursiyinsa can Sama,
Ya mai da su abin dariya.
5Ya yi musu magana da fushi,
Ya razanar da su da hasalarsa,
6Ya ce, “A bisa Sihiyona, dutsena tsattsarka,
Na naɗa sarkina.”
7 # A.M 13.33; Ibr 1.5; 5.5 Sarkin ya ce, “Zan yi shelar abin da Ubangiji ya hurta.
Ubangiji ya ce mini, ‘Kai ɗana ne,
Yau ne na zama mahaifinka.
8Ka yi roƙo, zan kuwa ba ka dukan al'ummai,
Dukan duniya kuma za ta zama taka.
9 # W.Yah 2.26,27; 12.5; 19.15 Za ka mallake su da sandan ƙarfe,
Za ka farfashe su kamar tukunyar yumɓu.’ ”
10Yanzu ku kasa kunne gare ni, ku sarakuna,
Ku mai da hankali, ku mahukunta!
11Ku bauta wa Ubangiji da tsoro,
Ku yi rawar jiki, ku rusuna masa,
12Ku yi mubaya'a da Ɗan,
Idan kuwa ba haka ba zai yi fushi da ku, za ku kuwa mutu,
Gama yakan yi fushi da sauri.
Albarka ta tabbata ga dukan masu zuwa gare shi neman mafaka!

Currently Selected:

Zab 2: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy