YouVersion Logo
Search Icon

Zab 4

4
Addu'ar Maraice ta Dogara ga Allah
1Ka amsa mini sa'ad da na yi kira,
Ya Allah, madogarata!
Lokacin da nake shan wahala, ka zama mai taimakona.
Ka yi mini alheri, ka kuma saurari addu'ata!
2Ku mutanen nan, sai yaushe za ku daina zagina?
Sai yaushe za ku daina ƙaunar abubuwan banza,
Da bin abin da yake na ƙarya?
3Ku tuna fa, Ubangiji ne ya zaɓe ni domin in zama nasa,
Ya kuma ji ni lokacin da na yi kira gare shi.
4 # Afi 4.26 Ku ji tsoro, ku daina aikata zunubinku,
Ku yi tunani da gaske a kan wannan
A kaɗaice, shiru, a ɗakunanku.
5Ku miƙa wa Ubangiji hadayun da suka dace,
Ku kuma dogara gare shi.
6Akwai mutane da yawa da suke cewa,
“Da ma a sa mana albarka!”
Ka dube mu da alheri, ya Ubangiji!
7Farin cikin da ka ba ni mai yawa ne,
Fiye da na waɗanda suke da wadataccen hatsi da ruwan inabi.
8Da zarar na kwanta, sai barci ya kwashe ni,
Kai kaɗai kake kiyaye ni sosai, ya Ubangiji.

Currently Selected:

Zab 4: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy