YouVersion Logo
Search Icon

Zab 1

1
LITTAFI NA FARI
(Zab 1—41)
Farin Ciki na Gaskiya
1Albarka ta tabbata ga mutumin da
Ba ya karɓar shawarar mugaye,
Wanda ba ya bin al'amuran masu zunubi,
Ko ya haɗa kai da masu wasa da Allah.
2Maimakon haka, yana jin daɗin karanta shari'ar Allah,
Yana ta nazarinta dare da rana.
3 # Irm 17.8 Yana kama da itacen da yake a gefen ƙorama,
Yakan ba da 'ya'ya a kan kari,
Ganyayensa ba sa yin yaushi,
Yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.
4Amma mugaye ba haka suke ba,
Su kamar yayi suke wanda iska take kwashewa.
5Allah kuwa zai hukunta mugaye,
Masu zunubi kuwa za a ware su daga adalai.
6Gama Ubangiji yana lura da al'amuran adalai,
Amma al'amuran mugaye za su watse.

Currently Selected:

Zab 1: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy