YouVersion Logo
Search Icon

Zab 149

149
Bari Isra'ilawa su Yabi Ubangiji
1Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji
Ku yabe shi cikin taron jama'arsa masu aminci!
2Ki yi murna, ke Isra'ila, sabili da Mahaliccinki,
Ku yi farin ciki, ku jama'ar Sihiyona, sabili da Sarkinku!
3Ku yabi sunansa, kuna taka rawa,
Ku kaɗa bandiri da garayu, kuna yabonsa.
4Ubangiji yana jin daɗin jama'arsa,
Yakan girmama mai tawali'u ya sa ya ci nasara.
5Bari jama'ar Allah su yi farin ciki saboda cin nasararsu,
Su raira waƙa don farin ciki.
6Bari su yi sowa da ƙarfi
Sa'ad da suke yabon Allah, da takubansu masu kaifi.
7Don su ci nasara bisa al'ummai,
Su kuma hukunta wa jama'a,
8Su ɗaure sarakunansu da sarƙoƙi,
Su ɗaure shugabanninsu da sarƙoƙin baƙin ƙarfe,
9Su hukunta wa al'ummai, kamar yadda Allah ya umarta.
Wannan shi ne cin nasarar jama'ar Allah!
Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

Currently Selected:

Zab 149: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in