YouVersion Logo
Search Icon

Zab 150

150
Ku Yabi Ubangiji
1Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
Ku yabi Allah a cikin Haikalinsa!
Ku yabi ƙarfinsa a sama!
2Ku yabe shi saboda manyan abubuwa
Waɗanda ya aikata!
Ku yabi mafificin girmansa!
3Ku yabe shi da kakaki!
Ku yabe shi da garayu da molaye!
4Ku yabe shi da bandiri kuna taka rawa!
Ku yabe shi da garayu da sarewa!
5Ku yabe shi da kuge!
Ku yabe shi da kuge masu amo!
6Ku yabi Ubangiji dukanku rayayyun talikai.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

Currently Selected:

Zab 150: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in