Zab 148
148
Bari dukan Halittar Allah su yi Yabonsa
1Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
Ku yabi Ubangiji daga sama,
Ku da kuke zaune a tuddan sama.
2Ku yabe shi dukanku mala'ikunsa,
Ku yabe shi, ku dukan rundunansa na sama!
3Ku yabe shi, ku rana da wata,
Ku yabe shi, ku taurari masu haskakawa!
4Ku yabe shi, ku sammai mafi tsayi duka!
Ku yabe shi, ku ruwayen da kuke bisa sararin sama!
5Bari su duka su yabi sunan Ubangiji!
Ya umarta, sai suka kasance.
6Ta wurin umarninsa aka kafa su
A wurarensu har abada,
Ba su kuwa da ikon ƙi.
7Ku yabi Ubangiji daga duniya,
Ku yabi Ubangiji, ku dodanin ruwa da dukan zurfafan teku.
8Ku yabe shi, ku walƙiya, da ƙanƙara, da dusar ƙanƙara,
Da gizagizai, da ƙarfafan iska waɗanda suke biyayya da umarnansa!
9Ku yabe shi, ku tuddai da duwatsu,
Da itatuwa 'ya'ya da kurama.
10Ku yabe shi dukanku dabbobi, na gida da na jeji,
Masu rarrafe da tsuntsaye!
11Ku yabe shi, ku sarakuna da dukan kabilai,
Ku yabe shi, ku shugabanni da dukan hukumomi.
12Ku yabe shi ku samari da 'yan mata!
Ku yabe shi, ku tsoffafi da yara!
13Bari dukansu su yabi sunan Ubangiji,
Sunansa ya fi dukan sauran sunaye girma,
Ɗaukakarsa kuwa tana bisa duniya da samaniya!
14Ya sa al'ummarsa ta yi ƙarfi,
Domin dukan jama'arsa su yabe shi
Jama'arsa Isra'ila, wadda yake ƙauna ƙwarai!
Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
Currently Selected:
Zab 148: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979