Zab 147
147
Yabon Alherin Allah a kan Urushalima
1Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
Abu mai kyau ne mu yabi Allahnmu,
Abu mai daɗi ne, daidai ne kuma, a yabe shi.
2Ubangiji yana rayar da Urushalima,
Yana komo da waɗanda aka kai su baƙunci a wata ƙasa.
3Yakan warkar da masu karyayyiyar zuciya,
Yakan ɗaure raunukansu.
4Ya ƙididdige yawan taurari,
Yakan kira kowanne da sunansa.
5Ubangijinmu mai girma ne, Mai Iko Dukka,
Saninsa ya fi gaban aunawa.
6Yakan ɗaukaka masu tawali'u,
Amma yakan ragargaza mugaye har ƙasa.
7Ku raira waƙar yabo ga Ubangiji,
Ku yabi Allah da garaya.
8Ya shimfiɗa gajimare a sararin al'arshi.
Ya tanada wa duniya ruwan sama,
Ya sa ciyayi su tsiro a kan tuddai.
9Yakan ba dabbobi abincinsu,
Yakan ciyar da 'ya'yan hankaki sa'ad da suka yi kuka gare shi.
10Ba ya jin daɗin ƙarfafan dawakai,
Ba ya murna da jarumawan mayaƙa.
11Amma yana jin daɗin waɗanda suke tsoronsa,
Yana jin daɗin waɗanda suke dogara da madawwamiyar ƙaunarsa.
12Ya Urushalima, ki yabi Ubangiji,
Ya Sihiyona, ki yabi Allahnki.
13Shi yake riƙe da ƙofofinki da ƙarfi,
Yakan sa wa jama'arki albarka.
14Yakan kiyaye kan iyakar ƙasarki lafiya,
Yakan kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.
15Yakan ba da umarni,
Nan da nan umarnin yakan iso duniya.
16Yakan aiko da dusar ƙanƙara mai kauri kamar ulu,
Ya watsa jaura kamar ƙura.
17Yakan aiko da ƙanƙara kamar duwatsu,
Ba wanda yake iya jurewa da sanyin da yakan aiko!
18Sa'an nan yakan ba da umarni,
Ƙanƙara kuwa ta narke,
Yakan aiko da iska, ruwa kuwa yakan gudu.
19Yana ba Yakubu saƙonsa,
Koyarwarsa da dokokinsa kuma ga Isra'ila.
20Bai yi wa sauran al'umma wannan ba,
Domin ba su san dokokinsa ba.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
Currently Selected:
Zab 147: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979