Zab 141
141
Addu'ar Maraice ta Neman Keɓewa daga Mugunta
1Ina kira gare ka, ya Ubangiji,
Ka taimake ni yanzu!
Ka saurare ni sa'ad da na kira gare ka.
2 #
W.Yah 5.8
Ka karɓi addu'ata kamar turaren ƙonawa,
Ka karɓi ɗaga hannuwa sama da na yi kamar hadayar maraice.
3Ya Ubangiji, ka sa a yi tsaron bakina,
Ka sa mai tsaro a leɓunana.
4Ka tsare ni daga son yin mugunta,
Ko kuma in haɗa kai da mugaye cikin muguntarsu,
Ka sa kada in taɓa yin tarayya da su a bukukuwansu!
5Nagarin mutum ya iya hukunta ni, ya tsauta mini da alheri,
Zai zamar mini kamar an shafe kaina da mai,
Domin kullayaumi ina addu'a gāba da mugayen ayyuka.
6Mutane za su yarda, cewa maganata gaskiya ce,
Sa'ad da aka jefo da masu mulkinsu ƙasa, daga ƙwanƙolin dutse,
7Kamar itacen da aka faskare, aka daddatse,
Haka aka watsar da ƙasusuwansu a gefen kabari.
8Amma ni, ya Ubangiji Allah, da nake dogara a gare ka,
Ina neman kiyayewarka,
Kada ka bar ni in halaka!
9Ka kiyaye ni daga tarkunan da suka kafa mini,
Daga ashiftar masu aikata mugunta.
10Ka sa mugaye su fāɗa cikin tarkunansu,
Ni kuwa in zo in wuce lafiya.
Currently Selected:
Zab 141: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979