Zab 140
140
Addu'ar Neman Tsari daga Mugaye
1Ka cece ni daga mugaye, ya Ubangiji,
Ka kiyaye ni daga mutane masu hargitsi.
2Kullum suna shirya mugunta,
Kullum suna kawo tashin hankali.
3 #
Rom 3.13
Harsunansu kamar macizai masu zafin dafi,
Kalmominsu kuwa kamar dafin gamsheƙa ne.
4Ka tsare ni daga ikon masu mugunta, ya Ubangiji,
Ka kiyaye ni daga masu tashin hankali,
Waɗanda suke shirya fāɗuwata.
5Masu girmankai sun kafa mini tarko,
Sun shimfiɗa ragar igiya,
Sun kuma kakkafa tarkuna a hanya don su kama ni.
6Na ce wa Ubangiji, “Kai ne Allahna.
Ka ji kukana na neman taimako, ya Ubangiji!
7Ya Ubangiji, Allahna, Mai Cetona, mai ƙarfi,
Kā kiyaye ni cikin yaƙi.
8Ya Ubangiji, kada ka biya wa mugaye burinsu,
Kada ka bar mugayen dabaru su yi nasara!
9“Kada ka bar maƙiyana su sami nasara,
Ka sa kashedin da suke yi mini yă koma kansu.
10Ka sa garwashin wuta yă zubo a kansu,
Ka sa a jefa su a rami, kada su ƙara fita.
11Ka sa waɗanda suke saran waɗansu a ƙaryace,
Kada su yi nasara.
Ka sa mugunta ta hallaka mutumin da yake ta da zaune tsaye.”
12Na sani kai, ya Ubangiji, kana kāre matsalar talakawa,
Da hakkin matalauta.
13Hakika adalai za su yabe ka,
Za su zauna a gabanka.
Currently Selected:
Zab 140: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979