YouVersion Logo
Search Icon

Zab 142

142
Addu'ar Neman Taimako
1Ina kira ga Ubangiji don neman taimako,
Ina roƙonsa.
2Na kawo masa dukan koke-kokena,
Na faɗa masa dukan wahalaina.
3Sa'ad da na yi niyyar fid da zuciya,
Ya san abin da zan yi.
A kan hanyar da zan bi
Maƙiyana sun kafa mini tarko a ɓoye.
4Na duba kewaye da ni, sai na ga ba ni da wanda zai taimake ni,
Ba wanda zai kiyaye ni,
Ba kuwa wanda ya kula da ni.
5Ya Ubangiji, na kawo kuka gare ka na neman taimako,
Ya Ubangiji, kai ne mai kiyaye ni,
Kai kaɗai nake so a rayuwata duka.
6Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako,
Gama na nutsa cikin fid da zuciya.
Ka cece ni daga maƙiyana
Waɗanda suka fi ƙarfina.
7Ka cece ni daga cikin wahalata,
Sa'an nan zan yabe ka cikin taron jama'arka,
Domin ka yi mini alheri.

Currently Selected:

Zab 142: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in