Zab 138
138
Godiya domin Alherin Ubangiji
1Da zuciya ɗaya nake gode maka, ya Ubangiji,
Ina raira waƙar yabonka a gaban alloli.
2Na durƙusa a gaban tsattsarkan Haikalinka
Ina yabon sunanka.
Sabili da madawwamiyar ƙaunarka da amincinka,
Saboda ka nuna ɗaukakarka da umarnanka.
3Ka amsa mini sa'ad da na yi kira gare ka,
Da ƙarfinka ka ƙarfafa ni.
4Dukan sarakunan duniyar nan za su yabe ka, ya Ubangiji,
Gama sun riga sun ji alkawaranka.
5Za su raira waƙa a kan abin da Ubangiji ya yi,
Za su raira waƙa kuma a kan ɗaukakarsa mai girma.
6Ko da yake Ubangiji yana can Sama,
Duk da haka yana kulawa da masu kaɗaici.
Masu girmankai kuwa ba za su iya ɓoye kansu daga gare shi ba.
7Ko lokacin da nake tsakiyar wahala,
Za ka kiyaye ni lafiya,
Ka yi gāba da abokan gābana, waɗanda suka husata,
Za ka kuwa cece ni da ikonka.
8Za ka aikata kowane abu da ka alkawarta mini,
Ya Ubangiji, ƙaunarka madawwamiya ce har abada.
Ka cikasa aikin da ka fara.
Currently Selected:
Zab 138: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979