YouVersion Logo
Search Icon

Zab 137

137
Kukan Isra'ilawa a Baƙuwar Ƙasa
1A bakin kogunan Babila
Muka zauna muka yi ta kuka,
Sa'ad da muka tuna da Sihiyona.
2A rassan itatuwan wardi da suke kusa da mu
Muka rataye garayunmu.
3Waɗanda suka kama mu suka sa mu mu yi waƙa,
Suka ce mana, “Ku yi mana shagali
Da waƙar da aka raira wa Sihiyona!”
4Kaƙa za mu raira waƙar Ubangiji
A baƙuwar ƙasa?
5Da ma kada in ƙara iya kaɗa garaya,
Idan na manta da ke, Urushalima!
6Da ma kada in ƙara iya raira waƙa,
Idan na manta da ke,
Idan ban tuna ke ce
Babbar abar farin ciki ba!
7Ka tuna, ya Ubangiji, da abin da Edomawa suka yi,
A ranar da aka ci Urushalima.
Ka tuna da yadda suka ce,
“A ragargaza ta har ƙasa!”
8 # W.Yah 18.6 Babila, za a hallaka ki!
Mai farin ciki ne shi wanda ya sāka miki
Bisa ga abin da kika yi mana.
9Mai farin ciki ne shi wanda zai kwashi jariranki
Yă fyaɗa su a kan duwatsu!

Currently Selected:

Zab 137: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in