YouVersion Logo
Search Icon

Zab 139

139
Cikakken Sanin Allah da Kulawarsa
1Ya Ubangiji, ka jarraba ni, ka san ni.
2Ka sa dukan abin da nake yi,
Tun daga can nesa ka gane dukan tunanina.
3Kana ganina, ko ina aiki, ko ina hutawa,
Ka san dukan ayyukana.
4Tun kafin in yi magana
Ka riga ka san abin da zan faɗa.
5Kana kewaye da ni a kowane sashe,
Ka kiyaye ni da ikonka.
6Yadda ka san ni ya fi ƙarfin magana,
Ya yi mini zurfi, ya fi ƙarfin ganewata.
7Ina zan tafi in tsere wa Ruhunka?
Ina zan gudu in tsere maka?
8Idan na hau cikin samaniya kana can,
In na kwanta a lahira kana can,
9In na tashi sama, na tafi, na wuce gabas,
Ko kuma na zauna a can yamma da nisa,
10Kana can domin ka bi da ni,
Kana can domin ka taimake ni.
11Da na iya roƙon duhu ya ɓoye ni,
Ko haske da yake kewaye da ni
Ya zama dare,
12Amma har duhun ma, ba duhu ba ne a gare ka,
Dare kuwa haskensa kamar na rana ne.
Duhu da haske, duk ɗaya ne gare ka.
13Kai ne ka halicci kowace gaɓa ta jikina,
Kai ne ka harhaɗa ni a cikin mahaifiyata.
14Ina yabonka gama kai abin tsoro ne,
Dukan abin da ka yi sabo ne, mai banmamaki.
Da zuciya ɗaya na san haka ne.
15Ka ga lokacin da ƙasusuwana suke siffatuwa,
Sa'ad da kuma ake harhaɗa su a hankali
A cikin mahaifiyata,
Lokacin da nake girma a asirce.
16Ka gan ni kafin a haife ni.
Ka ƙididdige kwanakin da ka ƙaddara mini,
Duka an rubuta su a littafinka,
Tun kafin faruwar kowannensu.
17Ya Allah, tunaninka suna da wuyar ganewa a gare ni,
Ba su da iyaka!
18In na ƙirga su, za su fi tsabar yashi,
Sa'ad da na farka, har yanzu ina tare da kai.
19Ya Allah, da yadda nake so ne, da sai ka karkashe mugaye!
'Yan ta da zaune tsaye kuma sai su rabu da ni!
20Suna ambaton mugayen abubuwa a kanka,
Suna faɗar mugayen abubuwa gāba da sunanka.
21Ya Ubangiji, ga yadda nake ƙin waɗanda suke ƙinka,
Da yadda nake raina waɗanda suke tayar maka!
22Ƙiyayyar da nake yi musu ta kai intaha,
Na ɗauke su, su abokan gābana ne.
23Jarraba ni, ya Allah, ka san tunanina,
Gwada ni, ka gane damuwata.
24Ka bincike, ko akwai wani rashin gaskiya a gare ni,
Ka bi da ni a madawwamiyar hanya.

Currently Selected:

Zab 139: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in