Zab 136
136
Waƙar Godiyar Ƙaunar Allah
1 #
1Tar 16.34; 2Tar 5.13; 7.3; Ezra 3.11; Zab 100.5; 106.1; 107.1; 118.1; Irm 33.11 Ku gode wa Ubangiji domin shi mai alheri ne,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
2Ku gode wa Allahn da ya fi dukan alloli girma,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
3Ku gode wa Ubangijin dukan iyayengiji,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
4Shi kaɗai ne yake aikata mu'ujizai masu girma,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
5 #
Far 1.1
Ta wurin hikimarsa ya halicci sammai,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
6 #
Far 1.2
Ya kafa duniya a bisa kan ruwa mai zurfi,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
7 #
Far 1.16
Shi ne ya halicci rana da wata,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce,
8Rana don ta yi mulkin yini,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce,
9Wata da taurari kuwa don su yi mulkin dare,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
10 #
Fit 12.29
Shi ya karkashe 'ya'yan fari maza, na Masarawa,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
11 #
Fit 12.51
Shi ya fito da jama'ar Isra'ila daga cikin Masar,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
12Da ƙarfinsa da ikonsa ya fito da su,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
13 #
Fit 14.21-29
Shi ne ya keta Bahar Maliya biyu,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
14Shi ya bi da jama'arsa ta cikin tekun,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
15Shi ne ya sa ruwa ya ci Fir'auna da rundunarsa,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
16Ya bi da jama'arsa cikin hamada,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
17Ya karkashe sarakuna masu iko,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
18Ya karkashe shahararrun sarakuna,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
19 #
L.Ƙid 21.21-30
Ya kashe Sihon, Sarkin Amoriyawa,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
20 #
L.Ƙid 21.31-35
Ya kashe Og, Sarkin Bashan,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
21Ya ba da ƙasarsu ga jama'arsa,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
22Ya ba da ita ga bawansa Isra'ila,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
23Bai manta da mu sa'ad da aka yi nasara da mu ba,
Gama ƙaunarsa madawwamiyar ce.
24Ya 'yantar da mu daga abokan gābanmu,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
25Yana ba da abinci ga dukan mutane da dabbobi,
Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
26Ku yi wa Allah sa Sama godiya,
Gama ƙaunarsa madawwamiyar ce.
Currently Selected:
Zab 136: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979