Zab 135
135
Waƙar Yabon Girman Ubangiji
1Ku yabi Ubangiji!
Ku yabi sunansa, ku bayin Ubangiji,
2Ku da kuke tsaye a Haikalin Ubangiji,
A wuri mai tsarki na Allahnmu.
3Ku yabi Ubangiji, domin nagari ne shi,
Ku raira yabbai ga sunansa, domin shi mai alheri ne.
4Ya zaɓar wa kansa Yakubu,
Jama'ar Isra'ila kuwa tasa ce.
5Na sani Ubangijinmu mai girma ne,
Ya fi dukan alloli girma.
6Yana aikata dukan abin da ya ga dama a Sama ko a duniya,
A tekuna, da kuma zurfafan da suke ƙarƙas.
7Yakan kawo gizagizan hadiri daga bangayen duniya,
Yakan yi walƙiya domin hadura,
Yakan fito da iska daga cikin taskarsa.
8A Masar ne ya karkashe 'ya'yan fari na mutane da na dabbobi.
9A can ne ya aikata mu'ujizai da al'ajabai,
Domin ya hukunta Fir'auna da dukan hukumar ƙasarsa.
10Ya hallakar da sauran al'umma masu yawa,
Ya karkashe sarakuna masu iko, wato
11Sihon, Sarkin Amoriyawa, da Og, Sarkin Bashan,
Da dukan sarakunan Kan'ana.
12Ya ba da ƙasarsu ga jama'arsa,
Ya ba da ita ga Isra'ila.
13Ya Ubangiji, kullayaumi mutane za su sani kai ne Allah,
Dukan tsararraki za su tuna da kai.
14Ubangiji zai ji juyayin mutanensa,
Zai 'yantar da bayinsa.
15 #
Zab 115.4-8; W.Yah 9.20 Gumakan al'ummai, da azurfa da zinariya aka yi su,
Hannuwan mutane ne suka siffata su.
16Suna da bakuna, amma ba sa magana,
Da idanu, amma ba sa gani.
17Suna da kunnuwa, amma ba sa ji,
Ba kuma numfashi a bakinsu.
18Ka sa su waɗanda suka yi su,
Da dukan waɗanda suke dogara gare su,
Su zama kamar gumakan da suka yi!
19Ku yabi Ubangiji, ya jama'ar Isra'ila,
Ku yabe shi, ya ku firistocin Allah!
20Ku yabi Ubangiji, ya ku Lawiyawa,
Ku yabe shi, dukanku da kuke tsoronsa!
21Ku yabi Ubangiji a Sihiyona da a Urushalima, wato a Haikalinsa.
Ku yabi Ubangiji!
Currently Selected:
Zab 135: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979