YouVersion Logo
Search Icon

Zab 122

122
Yabon Urushalima
1Na yi murna sa'ad da suka ce mini,
“Tashi mu tafi Haikalin Ubangiji!”
2Ga shi kuwa, mun iso,
Muna tsaye a ƙofofin Urushalima!
3Urushalima birni ce wadda aka maido ta yadda take dā,
Da kyakkyawan tsari, a shirye!
4A nan kabilai sukan zo,
Kabilan Isra'ila,
Domin su yi godiya ga Ubangiji,
Kamar yadda ya umarce su.
5A nan majalisu suke,
Wurin da sarki yake yi wa jama'arsa shari'a.
6Ku yi wa Urushalima addu'ar salama!
“Allah ya sa masu ƙaunarki su arzuta!
7Salama ta samu a garukanki,
Da zaman lafiya kuma a fādodinki.”
8Saboda abokaina da aminaina,
Na ce wa Urushalima, “Salama a gare ki!”
9Saboda Haikalin Ubangiji, Allahnmu,
Ina addu'a domin ki arzuta.

Currently Selected:

Zab 122: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in