Zab 123
123
Addu'ar Neman Jinƙai
1Ya Ubangiji, ina zuba ido gare ka,
A Sama inda kake mulki.
2Kamar yadda bara yake dogara ga maigidansa,
Baranya kuma ga uwargijiyarta,
Haka nan muke zuba ido gare ka, ya Ubangiji Allahnmu,
Har mu sami jinƙanka.
3Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai,
An gwada mana wulakanci matuƙa!
4Attajirai sun daɗe suna ta yi mana ba'a,
Azzalumai masu girmankai sun raina mu!
Currently Selected:
Zab 123: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979