YouVersion Logo
Search Icon

Zab 121

121
Ubangiji Ne Yake Kiyaye Ku
1Na duba wajen duwatsu,
Daga ina taimakona zai zo?
2Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,
Wanda ya yi sama da ƙasa.
3Ba zai bar ka ka fāɗi ba,
Makiyayinka, ba zai yi barci ba!
4Makiyayin Isra'ila,
Ba ya gyangyaɗi ko barci!
5Ubangiji zai lura da kai,
Yana kusa da kai domin ya kiyaye ka.
6Ba za ka sha rana ba,
Ko farin wata da dare.
7Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan hatsari,
Zai sa ka zauna lafiya.
8Zai kiyaye shigarka da fitarka,
Tun daga yanzu har abada.

Currently Selected:

Zab 121: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in