Zab 120
120
Addu'ar Neman Taimako
1Sa'ad da nake shan wahala,
Na yi kira ga Ubangiji,
Ya kuwa amsa mini.
2Ka cece ni, ya Ubangiji,
Daga maƙaryata da masu ruɗi!
3Ku maƙaryata, me Allah zai yi da ku?
Yaya zai hukunta ku?
4Da kibau masu tsini na mayaƙa,
Da garwashin wuta zai hukunta ku!
5Zama tare da ku mugun abu ne, kamar zama a Meshek,
Ko tare da mutanen Kedar!
6Na daɗe ƙwarai ina zama tare da mutane marasa son salama!
7Sa'ad da nake maganar salama,
Su sai su yi ta yaƙi.
Currently Selected:
Zab 120: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979