Zab 119
119
Mafificiyar Shari'ar Ubangiji
1Masu farin ciki ne, marasa laifi cikin zamansu,
Waɗanda suke zamansu bisa ga dokar Ubangiji.
2Masu farin ciki ne waɗanda suke bin umarnansa,
Waɗanda suke yi masa biyayya da zuciya ɗaya.
3Hakika ba su yin laifi,
Sukan yi tafiya a hanyoyin Ubangiji.
4Kai ka ba mu dokokinka,
Ka kuwa faɗa mana mu kiyaye su da aminci.
5Na sa zuciya zan yi aminci,
Game da kiyaye dokokinka!
6Idan na kula da dukan umarnanka,
To, ba zan kasa kaiwa ga burina ba.
7Zan yabe ka da tsattsarkar zuciya,
A sa'ad da na fahimci ka'idodinka masu adalci.
8Zan yi biyayya da dokokinka,
Ko kusa kada ka kashe ni!
Biyayya ga Shari'ar Ubangiji
9Ƙaƙa saurayi zai kiyaye ransa da tsarki?
Sai ta wurin biyayya da umarnanka.
10Da zuciya ɗaya nake ƙoƙarin bauta maka,
Ka kiyaye ni daga rashin biyayya da umarnanka!
11Na riƙe maganarka a zuciyata,
Don kada in yi maka zunubi.
12Ina yabonka, Ya Ubangiji,
Ka koya mini ka'idodinka!
13Zan ta da murya,
In maimaita dukan dokokin da ka bayar.
14Ina murna da bin umarnanka,
Fiye da samun dukiya mai yawa.
15Nakan yi nazarin umarnanka,
Nakan kuma yi bimbinin koyarwarka.
16Ina murna da dokokinka,
Ba zan manta da umarnanka ba.
Farin Ciki da Dokar Ubangiji
17Ka yi mini alheri, ni bawanka,
Domin in rayu in yi biyayya da koyarwarka.
18Ka buɗe idona
Domin in ga gaskiyar shari'arka mai banmamaki.
19Zamana a nan duniya na ɗan lokaci kaɗan ne.
Kada ka ɓoye mini umarnanka!
20Zuciyata ta ƙosa saboda marmari,
A kowane lokaci ina so in san hukuntanka.
21Kakan tsauta wa masu girmankai,
La'anannu ne waɗanda suka ƙi bin umarnanka.
22Ka kuɓutar da ni daga cin mutuncinsu da raininsu,
Domin na kiyaye dokokinka.
23Ko da sarakuna za su taru
Su shirya mini maƙarƙashiya,
Duka da haka, ni bawanka,
Zan yi nazarin ka'idodinka.
24Umarnanka suna faranta mini rai,
Su ne mashawartana.
Ƙudurin yin Biyayya ga Dokar Ubangiji
25Ina kwance cikin ƙura, an yi nasara da ni,
Ka wartsakar da ni kamar yadda ka alkawarta!
26Na hurta dukan abin da na aikata, ka kuwa amsa mini,
Ka koya mini ka'idodinka!
27Ka koya mini yadda zan yi biyayya da dokokinka,
In kuma yi nazarin koyarwarka mai banmamaki.
28Ɓacin rai ya ci ƙarfina,
Ka ƙarfafa ni, kamar yadda ka alkawarta.
29Ka kiyaye ni daga bin muguwar hanya,
Ta wurin alherinka, ka koya mini dokarka.
30Na yi niyya in yi biyayya,
Na mai da hankali ga ka'idodinka.
31Na bi umarnanka, ya Ubangiji,
Kada ka sa in kasa ci wa burina!
32Ina ɗokin yin biyayya da umarnanka,
Gama za ka ƙara mini fahimi.
Addu'ar Neman Fahimi
33Ka koya mini ma'anar dokokinka, ya Ubangiji,
Zan kuwa yi biyayya da su a kowane lokaci.
34Ka fassara mini dokarka, ni kuwa zan yi biyayya da ita,
Zan kiyaye ta da zuciya ɗaya.
35Ka bishe ni a hanyar umarnanka,
Domin a cikinsu nakan sami farin ciki
36Ka sa ni in so yin biyayya da ka'idodinka,
Fiye da samun dukiya.
37Ka kiyaye ni daga mai da hankali ga abin da yake marar amfani,
Ka yi mini alheri kamar yadda ka alkawarta.
38Ka tabbatar da alkawarin da ka yi mini, ni bawanka,
Irin wanda kakan yi wa waɗanda suke tsoronka.
39Ka kiyaye ni daga cin mutuncin da nake tsoro,
Ka'idodinka suna da amfani ƙwarai!
40Ina so in yi biyayya da umarnanka,
Gama kai mai adalci ne,
Ka yi mini alheri!
Dogara ga Dokar Ubangiji
41Ka nuna mini yawan ƙaunar da kake yi mini, ya Ubangiji,
Ka cece ni bisa ga alkawarinka.
42Sa'an nan zan amsa wa waɗanda suke cin mutuncina,
Domin na dogara ga maganarka.
43Ka ba ni iko in iyar da saƙonka na gaskiya a kowane lokaci,
Gama sa zuciyata tana ga hukuntanka.
44Kullum zan yi biyayya da dokarka har abada abadin!
45Zan rayu da cikakken 'yanci,
Gama na yi ƙoƙari in kiyaye ka'idodinka.
46Zan hurta umarnanka ga sarakuna,
Ba kuwa zan ji kunya ba.
47Ina murna in yi biyayya da umarnanka,
Saboda in ƙaunarsu.
48Ina girmama umarnanka, ina kuwa ƙaunarsu,
Zan yi ta tunani a kan koyarwarka.
Amincewa da Shari'ar Ubangiji
49Ka tuna da alkawarin da ka yi mini, ni bawanka,
Ka ƙarfafa zuciyata.
50Ko ina shan wahala, ana ta'azantar da ni,
Saboda alkawarinka yana rayar da ni.
51Masu girmankai suna raina ni,
Amma ban rabu da dokarka ba.
52Na tuna da koyarwar da ka yi mini a dā,
Sukan kuwa ta'azantar da ni, ya Ubangiji.
53Haushi ya kama ni sosai,
Sa'ad da na ga mugaye suna keta dokarka.
54Ina zaune can nesa da gidana na ainihi,
Sai na ƙago waƙoƙi a kan umarnanka.
55Da dare nakan tuna da kai, ya Ubangiji,
Ina kuwa kiyaye dokarka.
56Wannan shi ne farin cikina,
In yi biyayya da umarnanka.
Tunani a kan Shari'ar Ubangiji
57Kai kaɗai nake so, ya Ubangiji,
Na yi alkawari in yi biyayya da dokokinka.
58Ina roƙonka da zuciya ɗaya,
Ka yi mini jinƙai kamar yadda ka alkawarta!
59Na yi tunani a kan ayyukana,
Na yi alkawari in bi ka'idodinka.
60Ba tare da ɓata lokaci ba,
Zan gaggauta in kiyaye umarnanka.
61Mugaye sun ɗaure ni tam da igiyoyi,
Amma ba zan manta da dokarka ba.
62Da tsakar dare nakan farka,
In yabe ka saboda hukuntanka masu adalci.
63Ina abuta da duk waɗanda suke bauta maka,
Da duk waɗanda suke kiyaye dokokinka.
64Ya Ubangiji, duniya ta cika da madawwamiyar ƙaunarka,
Ka koya mini umarnanka!
Amfanin Shari'ar Ubangiji
65Kana cika alkawarinka, ya Ubangiji,
Kana kuwa yi mini alheri, ni bawanka.
66Ka ba ni hikima da ilimi
Domin ina dogara ga umarnanka.
67Kafin ka hore ni nakan yi kuskure,
Amma yanzu ina biyayya da maganarka.
68Managarci ne kai, mai alheri ne kuma,
Ka koya mini umarnanka!
69Masu girmankai sun faɗi ƙarairayi a kaina,
Amma da zuciya ɗaya nake biyayya da ka'idodinka.
70Waɗannan mutane ba su da ganewa,
Amma ni ina murna da dokarka.
71Horon da aka yi mini ya yi kyau,
Domin ya sa na koyi umarnanka.
72Dokar da ka yi
Muhimmiya ce a gare ni,
Fiye da dukan dukiyar duniya.
Adalcin Shari'ar Ubangiji
73Kai ne ka halicce ni, ka kuma kiyaye ni lafiya,
Ka ba ni ganewa, don in koyi dokokinka.
74Waɗanda suke tsoronka za su yi murna sa'ad da suka gan ni,
Saboda ina dogara ga alkawarinka.
75Na sani ka'idodinka na adalci ne, ya Ubangiji,
Ka hore ni, domin kai mai aminci ne.
76Ka sa madawwamiyar ƙaunarka ta ta'azantar da ni,
Kamar yadda ka alkawarta mini, ni bawanka.
77Ka yi mini jinƙai, zan rayu,
Saboda ina murna da dokarka.
78Ka kunyatar da masu girmankai
Saboda sun ba da shaidar zur a kaina,
Amma ni, zan yi tunani a kan ka'idodinka.
79Ka sa waɗanda suke tsoronka su zo gare ni,
Da waɗanda suka san umarnanka.
80Ka sa in yi cikakkiyar biyayya da umarnanka,
Sa'an nan zan tsere wa shan kunyar faɗuwa.
Addu'ar Neman Ceto
81Na tafke, ya Ubangiji, jira nake ka cece ni,
Na dogara ga maganarka.
82Idanuna sun gaji da zuba ido ga alkawarinka.
Roƙo nake, “Sai yaushe za ka taimake ni?”
83Na zama marar amfani kamar salkar ruwan inabi wanda aka jefar da ita,
Duk da haka ban manta da umarnanka ba.
84Har yaushe zan yi ta jira?
Yaushe za ka yi wa waɗanda suke tsananta mini hukunci?
85Masu girmankai, waɗanda ba su biyayya da dokarka,
Sun haƙa wushefe don su kama ni.
86Umarnanka duka, abin dogara ne,
Mutane suna tsananta mini da ƙarairayi,
Ka taimake ni!
87Sun kusa ci wa burinsu na su kashe ni,
Amma ban raina ka'idodinka ba.
88Saboda madawwamiyar ƙaunarka, ka yi mini alheri,
Domin in yi biyayya da dokokinka.
Gaskata Shari'ar Ubangiji
89Maganarka tabbatacciya ce, ya Ubangiji,
A kafe take a Sama.
90Amincinka ya tabbata har abada,
Ka kafa duniya a inda take, tana nan kuwa a wurin.
91Dukan abubuwa suna nan har wa yau saboda umarninka,
Domin su duka bayinka ne.
92Da ba domin dokarka ita ce sanadin farin cikina ba,
Da na mutu saboda hukuncin da na sha.
93Faufau ba zan raina ka'idodinka ba,
Gama saboda su ka bar ni da rai.
94Ni naka ne, ka cece ni!
Na yi ƙoƙari in yi biyayya da umarnanka.
95Mugaye suna jira su kashe ni,
Amma zan yi ta tunani a kan dokokinka.
96Na koya cewa ba wani abu da yake cikakke,
Amma umarninka ba shi da iyaka.
Ƙaunar Shari'ar Ubangiji
97Ga yadda nake ƙaunar dokarka!
Ina ta tunani a kanta dukan yini.
98Umarninka yana tare da ni a kowane lokaci,
Ya sa ni in yi hikima fiye da dukan maƙiyana.
99Ganewata ta fi ta dukan malamaina,
Saboda ina ta tunani a kan koyarwarka.
100Na fi tsofaffi hikima,
Saboda ina biyayya da umarnanka.
101Nakan guje wa halin mugunta
Saboda ina so in yi biyayya da maganarka.
102Ban raina koyarwarka ba
Saboda kai ne ka koya mini.
103Ɗanɗanon ka'idodinka akwai zaƙi,
Har sun fi zuma zaƙi!
104Na ƙaru da hikima daga dokokinka,
Saboda haka ina ƙin dukan halin da yake ba daidai ba.
Haske daga Shari'ar Ubangiji
105Maganarka fitila ce wadda za ta bi da ni,
Haske ne kuma a kan hanyata.
106Zan cika muhimmin alkawarina,
In yi biyayya da koyarwarka mai adalci.
107Azabaina, ya Ubangiji, suna da yawa,
Ka rayar da ni kamar yadda ka alkawarta!
108Ka karɓi addu'ata ta godiya, ya Ubangiji,
Ka koya mini umarnanka.
109Kullum a shirye nake in kasai da raina,
Ban manta da umarninka ba.
110Mugaye sun kafa mini tarko,
Amma ban yi rashin biyayya da umarnanka ba.
111Umarnanka nawa ne har abada, Su ne murnar zuciyata.
112Na ƙudura zan yi biyayya da ka'idodinka,
Har ranar mutuwata.
Akwai Lafiya ga Bin Shari'ar Ubangiji
113Ina ƙin waɗanda ba su yi maka aminci,
Amma ina ƙaunar dokarka.
114Kai ne kake kāre ni, kake kuma kiyaye ni,
Ina sa zuciya ga alkawarinka.
115Ku rabu da ni, ku masu zunubi!
Zan yi biyayya da umarnan Allahna.
116Ka ƙarfafa ni kamar yadda ka alkawarta, zan kuwa rayu,
Kada ka bar ni in kasa ci wa burina!
117Ka riƙe ni, sai in zauna lafiya,
Koyaushe zan mai da hankali ga umarnanka.
118Ka rabu da dukan waɗanda ba su biyayya da dokokinka,
Dabarunsu na yaudara banza ne.
119Kakan yi banza da duk mai mugunta,
Don haka ina ƙaunar koyarwarka.
120Saboda kai, nake jin tsoro,
Na cika da tsoro saboda shari'unka.
Biyayya da Shari'ar Ubangiji
121Na yi abin da yake daidai mai kyau,
Kada ka bar ni a hannun maƙiyana!
122Sai ka yi alkawari za ka taimaki bawanka,
Kada ka bar masu girmankai su wahalshe ni!
123Idanuna sun gaji da duban hanyar cetonka,
Ceton da ka alkawarta.
124Ka bi da ni bisa ga tabbatacciyar ƙaunarka,
Ka koya mini umarnanka.
125Ni bawanka ne, don haka ka ba ni ganewa,
Don in san koyarwarka.
126Ya Ubangiji, lokaci ya yi da za ka yi wani abu,
Saboda mutane sun ƙi yin biyayya da dokarka!
127Ina ƙaunar umarnanka, fiye da zinariya,
Fiye da zinariya tsantsa.
128Saboda haka ina bin dukan koyarwarka,
Ina kuwa ƙin dukan mugayen al'amura.
Niyyar yin Biyayya da Shari'ar
129Koyarwarka tana da ban al'ajabi,
Da zuciya ɗaya nake biyayya da su.
130Fassarar koyarwarka takan ba da haske,
Takan ba da hikima ga wanda bai ƙware ba.
131Ina haki da baki a buɗe,
Saboda marmarin da nake yi wa umarnanka.
132Ka juyo wurina ka yi mini jinƙai,
Kamar yadda kakan yi wa masu ƙaunarka.
133Kada ka bar ni in fāɗi kamar yadda ka alkawarta,
Kada ka bar mugunta ta rinjaye ni.
134Ka cece ni daga waɗanda suke zaluntata,
Domin in yi biyayya da umarnanka.
135Ka sa mini albarka da kasancewarka tare da ni,
Ka koya mini dokokinka.
136Hawayena suna malalowa kamar kogi,
Saboda jama'a ba su biyayya da shari'arka ba.
Adalcin Shari'ar Ubangiji
137Kai mai adalci ne, ya Ubangiji,
Dokokinka kuma daidai ne,
138Ka'idodin da ka bayar kuwa dukansu masu kyau ne,
Daidai ne kuwa.
139Fushi yana cina kamar wuta,
Saboda maƙiyana ba su kula da umarnanka ba.
140Alkawarinka ba ya tashi!
Bawanka yana ƙaunar alkawarinka ƙwarai!
141Ni ba kome ba ne, rainanne ne,
Amma ban ƙi kula da ka'idodinka ba.
142Adalcinka zai tabbata har abada,
Dokarka gaskiya ce koyaushe.
143A cike nake da wahala da damuwa,
Amma umarnanka suna faranta zuciyata.
144Koyarwarka masu adalci ne har abada,
Ka ba ni ganewa domin in rayu.
Addu'ar Neman Kuɓutarwa
145Ina kira gare ka da zuciya ɗaya,
Ka amsa mini, ya Ubangiji,
Zan yi biyayya da umarnanka!
146Ina kira gare ka,
Ka cece ni, zan bi ka'idodinka!
147Tun kafin fitowar rana ina kira gare ka neman taimako,
Na sa zuciya ga alkawarinka.
148Dare farai ban yi barci ba,
Ina ta bimbini a kan koyarwarka.
149Ka ji ni, ya Ubangiji, bisa ga madawwamiyar ƙaunarka,
Ka kiyaye raina bisa ga alherinka!
150Mugayen nan waɗanda suke tsananta mini sun matso kusa,
Mutanen da ba su taɓa kiyaye dokarka ba.
151Amma kana kusa da ni, ya Ubangiji,
Dukan alkawaranka gaskiya ne.
152Tuntuni na ji labarin koyarwarka,
Ka sa su tabbata har abada.
Roƙo domin Ceto
153Ka dubi wahalata, ka cece ni,
Gama ban ƙi kulawa da dokarka ba.
154Ka kāre manufata, ka kuɓutar da ni,
Ka cece ni kamar yadda ka alkawarta!
155Ba za a ceci mugaye ba,
Saboda ba su yi biyayya da dokokinka ba.
156Amma juyayinka yana da girma, ya Ubangiji,
Saboda haka ka cece ni yadda ka yi niyya.
157Maƙiyana da masu zaluntata, suna da yawa,
Amma ban fasa yin biyayya da dokokinka ba.
158Sa'ad da na dubi waɗannan maciya amana,
Sai in ji ƙyama ƙwarai,
Domin ba su yi biyayya da umarninka ba.
159Ka dubi yadda nake ƙaunar koyarwarka, ya Ubangiji!
Ka cece ni bisa ga madawwamiyar ƙaunarka.
160Cibiyar dokarka gaskiya ce,
Dukan ka'idodinka na adalci tabbatattu ne.
Duƙufa da Bin Dokar Ubangiji
161Ƙarfafan mutane sun auka mini ba dalili,
Amma maganarka ce nake girmamawa.
162In farin ciki ƙwarai saboda alkawaranka,
Farin cikina kamar na wanda ya sami dukiya mai yawa ne.
163Ina ƙin ƙarairayi, ba na jin daɗinsu,
Amma ina ƙaunar dokarka.
164A kowace rana nakan gode maka sau bakwai,
Saboda shari'unka masu adalci ne.
165Waɗanda suke ƙaunar dokarka sun sami cikakken zaman lafiya,
Ba wani abin da zai sa su fāɗi.
166Ina jiranka ka cece ni, ya Ubangiji,
Ina aikata abin da ka umarta.
167Ina biyayya da ka'idodinka,
Ina ƙaunarsu da zuciya ɗaya.
168Ina biyayya da umarnanka da koyarwarka,
Kana kuwa ganin dukan abin da nake yi.
Addu'ar Neman Taimako
169Bari kukana yă kai gare ka, ya Ubangiji!
Ka ganar da ni kamar yadda ka alkawarta.
170Bari addu'ata ta zo gare ka,
Ka cece ni kamar yadda ka alkawarta!
171Zan yabe ka kullayaumin
Domin ka koya mini ka'idodinka.
172Zan raira waƙa a kan alkawarinka,
Domin umarnanka a gaskiya ne.
173Kullum a shirye kake domin ka taimake ni,
Saboda ina bin umarnanka.
174Ina sa zuciya ga cetonka ƙwarai, ya Ubangiji!
Ina samun farin ciki ga dokarka.
175Ka rayar da ni don in yabe ka,
Ka sa koyarwarka su taimake ni!
176Ina kai da kawowa kamar ɓatacciyar tunkiya,
Ka zo ka neme ni, ni bawanka,
Saboda ban ƙi kulawa da dokokinka ba.
Currently Selected:
Zab 119: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979