Zab 118
118
Addu'ar Godiyar domin Cin Nasara
1 #
1Tar 16.34; 2Tar 5.13; 7.3; Ezra 3.11; Zab 100.5; 106.1; 107.1; 136.1; Irm 33.11 Ku gode wa Ubangiji,
Domin shi mai alheri ne,
Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.
2Bari jama'ar Isra'ila su ce,
“Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”
3Bari dukan firistoci na Allah su ce,
“Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”
4Bari dukan waɗanda suke tsoronsa su ce,
“Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”
5A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji
Ya kuwa amsa mini, ya kuɓutar da ni.
6 #
Ibr 13.6
Ubangiji yana tare da ni, ba zan ji tsoro ba.
Me mutane za su iya yi mini?
7Ubangiji ne yake taimakona,
Zan kuwa ga fāɗuwar maƙiyana da idona.
8Gwamma a dogara ga Ubangiji,
Da a dogara ga mutane.
9Gwamma a dogara ga Ubangiji,
Da a dogara ga shugabanni na mutane kawai.
10Ma ƙiya da yawa sun kewaye ni,
Amma na hallaka su ta wurin ikon Ubangiji!
11Suka kewaye ni a kowane gefe
Amma na hallaka su ta wurin ikon Ubangiji!
12Suka rufe ni kamar ƙudan zuma,
Amma suka ƙone nan da nan kamar wutar jeji,
Ta wurin ikon Ubangiji na hallaka su!
13Aka auko mini da tsanani,
Har aka kore ni,
Amma Ubangiji ya taimake ni.
14 #
Fit 15.2; Ish 12.2 Ubangiji yakan ba ni iko, ya ƙarfafa ni,
Shi ne Mai Cetona!
15Ku kasa kunne ga sowar murna ta nasara
A cikin alfarwan jama'ar Allah.
“Ikon Ubangiji mai girma ne ya aikata wannan!
16Ikonsa ne ya kawo mana nasara,
Babban ikonsa a wurin yaƙi!”
17Ba zan mutu ba, amma rayuwa zan yi,
Don in ba da labarin abin da Ubangiji ya yi.
18Ya hukunta ni da hukunci mai tsanani,
Amma bai kashe ni ba.
19A buɗe mini ƙofofin Haikali,
Zan shiga ciki in yabi Ubangiji!
20Wannan ƙofar Ubangiji ce,
Sai adalai kaɗai suke shiga ciki!
21Ina yabonka, ya Ubangiji, domin ka ji ni,
Domin ka ba ni nasara!
22 #
Luk 20.17; A.M 4.11; 1Bit 2.7 #
Mat 21.42; Mar 12.10,11 Dutsen da magina suka ƙi, wai ba shi da amfani,
Sai ya zama shi ya fi duka amfani.
23Ubangiji ne ya yi haka,
Wannan kuwa abin banmamaki ne!
24Wace irin rana ce haka da Ubangiji ya ba mu!
Bari mu yi farin ciki, mu yi biki!
25 #
Mat 21.9; Mar 11.9; Yah 12.13 Ka cece mu, ya Ubangiji, ka cece mu!
Ka ba mu nasara, ya Ubangiji!
26 #
Mat 21.9; 23.39; Mar 11.9; Luk 13.35; 19.38; Yah 12.13 Allah yakan sa wa wanda ya zo da sunan Ubangiji albarka!
Daga Haikalin Ubangiji muke yabonka!
27Ubangiji shi ne Allah, yana yi mana alheri,
Ku ɗauki hadayunku ku yi ta idi,
Ku ɗaura su a zankayen bagade.
28Kai ne Allahna, kai nake yi wa godiya,
Zan yi shelar girmanka.
29Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne,
Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.
Currently Selected:
Zab 118: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979