YouVersion Logo
Search Icon

Zab 107

107
LITTAFI NA BIYAR
(Zab 107—150)
Ubangiji Ne Mai Kuɓutarwa daga Wahala
1 # 1Tar 16.34; 2Tar 5.13; 7.3; Ezra 3.11; Zab 100.5; 106.1; 118.1; 136.1; Irm 33.11 Ku gode wa Ubangiji, gama shi nagari ne,
Ƙaunarsa madawwamiya ce!
2Ku zo mu yabi Ubangiji tare,
Dukanku waɗanda ya fansa,
Gama ya ƙwato ku daga maƙiyanku.
3Ya komo da ku daga ƙasashen waje,
Daga gabas da yamma, kudu da arewa.
4Waɗansu suka yi ta kai da kawowa a hamada inda ba hanya,
Sun kasa samun hanyar da za ta kai su garin da za su zauna a ciki.
5Suka yi ta fama da yunwa, da ƙishirwa,
Suka fid da zuciya ga kome.
6Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,
Ya kuwa cece su daga wahalarsu.
7Ya fisshe su, ya bi da su sosai,
Zuwa birnin da za su zauna.
8Dole ne su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa,
Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu!
9Ya shayar da waɗanda suke jin ƙishirwa,
Ya kuma ƙosar da mayunwata da alheransa.
10Waɗansu suna zaune cikin duhu da inuwar mutuwa,
'Yan sarƙa suna shan wahala da sarƙoƙi,
11Saboda sun tayar, sun ƙi bin umarnan Allah Maɗaukaki,
Sun kuwa ƙi koyarwarsa.
12Suka gaji tiƙis saboda tsananin aiki,
Za su faɗi ƙasa, ba mataimaki.
13A cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,
Ya kuwa cece su daga wahalarsu.
14Ya fisshe su daga cikin duhu da inuwar mutuwa,
Ya tsintsinka sarƙoƙinsu.
15Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa,
Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.
16Ya kakkarya ƙofofin da aka yi da tagulla.
Ya kuma ragargaza ƙyamaren da aka yi da baƙin ƙarfe.
17Waɗansu suka yi ciwo sabili da zunubansu,
Suna ta shan wahala saboda muguntarsu.
18Ba su so su ga abinci,
Sun kusa mutuwa.
19A cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,
Ya kuwa cece su daga azabar da suke sha.
20Da umarninsa ya warkar da su,
Ya cece su daga kabari.
21Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa,
Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.
22Dole su gode masa, su miƙa masa hadayu,
Su raira waƙoƙin murna,
Su faɗi dukan abin da ya yi!
23Waɗansu suka yi tafiya a teku da jirage,
Suna samun abin zaman garinsu daga tekuna.
24Suka ga abin da Ubangiji ya aikata,
Ayyukansa masu banmamaki waɗanda ya yi a tekuna.
25Ya ba da umarni, sai babbar iska ta tashi,
Ta fara hurowa, ta sa raƙuman ruwa su tashi.
26Aka ɗaga jiragen ruwa sama,
Sa'an nan suka tsinduma cikin zurfafa.
Da mutanen suka ga irin hatsarin da suke ciki,
Sai zuciyarsu ta karai.
27Suka yi ta tuntuɓe suna ta tangaɗi kamar bugaggu,
Gwanintarsu duka ta zama ta banza.
28Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,
Ya kuwa cece su daga azabarsu.
29Ya sa hadiri ya yi tsit,
Raƙuman ruwa kuma suka yi shiru.
30Suka yi murna saboda wurin ya yi shiru,
Ya kuma kai su kwatar jiragen ruwa lafiya,
Wurin da suke so.
31Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa,
Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.
32Dole su yi shelar girmansa cikin taron jama'a,
Su kuma yabe shi a gaban majalisar dattawa.
33Ubangiji ya sa koguna suka ƙafe ƙaƙaf,
Ya hana maɓuɓɓugai su gudana.
34Ya mai da ƙasa mai dausayi ta zama mai gishiri, marar amfani,
Saboda muguntar waɗanda suke zaune a can.
35Ya sāke hamada ta zama tafkunan ruwa,
Ya kuma mai da busasshiyar ƙasa ta zama maɓuɓɓugai masu gudana.
36Ya bar mayunwata su zauna a can,
Suka kuwa gina birni don su zauna a ciki.
37Suka shuka gonaki suka dasa kurangar inabi,
Waɗanda suka ba da amfani mai yawan gaske.
38Ya sa wa jama'arsa albarka,
Suka kuwa haifi 'ya'ya da yawa.
Bai bar garkunan shanunsu su ragu ba.
39Sa'ad da aka ci nasara a kan jama'ar Allah,
Aka ƙasƙantar da su ta wurin mugun zalunci,
Da wahalar da aka yi musu.
40Sai Allah ya wulakanta waɗanda suka zalunci jama'arsa.
Ya sa su suka yi ta kai da kawowa
A hamada inda ba hanya.
41Ya tsamo masu bukata daga cikin baƙin cikinsu,
Ya sa iyalansu su riɓaɓɓanya kamar garkunan tumaki.
42Da adalai suka ga wannan, sai suka yi murna,
Mugaye kuwa aka rufe bakinsu.
43Da ma a ce masu hikima
Za su yi tunani a kan waɗannan abubuwa,
Da ma kuma su yarda
Da madawwamiyar ƙaunar Ubangiji.

Currently Selected:

Zab 107: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in