YouVersion Logo
Search Icon

Zab 108

108
Addu'ar Neman Tsari daga Maƙiya
(Zab 57.7-11; 60.5-12)
1A shirye nake, ya Allah,
Na shirya sosai!
Zan raira waƙa in yabe ka!
Ka farka, ya raina!
2Ku farka, ya molona da garayata!
Zan farkar da rana!
3Zan yi maka godiya a tsakiyar sauran al'umma, ya Ubangiji!
Zan yabe ka a tsakiyar kabilai!
4Madawwamiyar ƙaunarka ta kai har can saman sammai,
Amincinka kuma ya kai sararin sammai.
5Ya Allah, ka bayyana girmanka a sararin sama,
Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!
6Ka cece mu da ƙarfinka, ka amsa addu'ata,
Domin jama'ar da kake ƙauna ta sami cetonka.
7A tsattsarkan wurinsa, Allah ya faɗa ya ce,
“Da nasara zan raba Shekem,
Da nasara kuma zan rarraba Sukkot ga jama'ata.
8Gileyad tawa ce, har da Manassa ma,
Ifraimu ne kwalkwalina,
Yahuza kuma sandana ne na sarauta.
9Amma zan yi amfani da Mowab kamar kwanon wanki,
Edom kuwa kamar akwatin takalmina.
Zan yi sowar nasara a kan Filistiyawa.”
10Ya Allah, wa zai kai ni birni mai kagara?
Wa zai kai ni Edom?
11Da gaske ka yashe mu ke nan?
Ba za ka yi tafiya
Tare da sojojinmu ba?
12Ka taimake mu, mu yaƙi abokin gāba,
Domin taimako irin na mutum banza ne!
13Idan Allah yana wajenmu,
Za mu yi nasara,
Zai kori abokan gābanmu.

Currently Selected:

Zab 108: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in