YouVersion Logo
Search Icon

Zab 106

106
Tawayen Isra'ila
1 # 1Tar 16.34; 2Tar 5.13; 7.3; Ezra 3.11; Zab 100.5; 107.1; 118.1; 136.1; Irm 33.11 Ku yabi Ubangiji!
Ku yi wa Ubangiji godiya, gama nagari ne shi,
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
2Wa zai iya faɗar dukan manya manyan ayyuka da ya yi?
Wa zai iya yi masa isasshen yabo?
3Masu farin ciki ne waɗanda suke biyayya da umarnansa,
Waɗanda kullayaumi suke aikata abin da yake daidai!
4Ka tuna da ni sa'ad da za ka taimaki jama'arka, ya Ubangiji!
Ka sa ni cikinsu, sa'ad da za ka cece su.
5Ka yardar mini in ga wadatar jama'arka,
In yi tarayya da jama'arka da farin cikinsu,
In yi farin ciki tare da waɗanda suke murna ta fāriya domin su naka ne.
6Mun yi zunubi yadda kakanninmu suka yi,
Mugaye ne, mun aikata mugunta.
7 # Fit 14.10-12 Kakanninmu a Masar
Ba su fahimci ayyukan Allah masu banmamaki ba,
Sau da yawa sukan manta da irin ƙaunar da ya nuna musu,
Suka tayar wa Mai Iko Dukka a Bahar Maliya.
8Amma duk da haka ya cece su, kamar yadda ya alkawarta,
Domin ya nuna ikonsa mai girma.
9 # Fit 14.21-31 Ya tsauta wa Bahar Maliya, ta ƙafe,
Har ya bi da jama'arsa su haye
Kamar a bisa busasshiyar ƙasa.
10Ya cece su daga maƙiyansu,
Ya ƙwato su daga wurin abokan gābansu.
11Ruwa ya cinye maƙiyansu,
Ba wanda ya tsira.
12 # Fit 15.1-21 Sa'an nan jama'arsa suka gaskata alkawarinsa,
Suka raira yabo gare shi.
13Amma nan da nan, suka manta da abin da ya yi,
Suka aikata, ba su jira shawararsa ba.
14 # L.Ƙid 11.4-34 Suka cika da sha'awa cikin hamada,
Suka jarraba Allah,
15Sai ya ba su abin da suka roƙa,
Amma ya aukar musu da muguwar cuta.
16 # L.Ƙid 16.1-35 Can cikin hamada suka ji kishin Musa
Da Haruna, bayin Ubangiji, tsarkaka,
17Sai ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan,
Ta binne Abiram da iyalinsa.
18Wuta ta sauko bisa magoya bayansu,
Ta ƙone mugayen mutanen nan.
19 # Fit 32.1-14 Suka ƙera ɗan maraƙi da zinariya a Horeb,
Suka yi masa sujada.
20Suka musaya ɗaukakar Allah
Da siffar dabba mai cin ciyawa.
21Suka manta da Allah wanda ya cece su,
Ta wurin manyan ayyuka da ya yi a Masar.
22Kai, Allah ya aikata abubuwa masu ban al'ajabi a can!
Ga kuma abubuwa masu banmamaki da ya aikata a Bahar Maliya!
23Saboda wannan Allah ya ce zai hallaka jama'arsa,
Amma Musa, zaɓaɓɓen bawansa, ya yi godo ga Allah,
Allah kuwa ya huce, bai hallaka su ba.
24 # L.Ƙid 14.1-35 Sai suka ƙi ƙasan nan mai ni'ima,
Saboda ba su gaskata alkawarin Allah ba.
25Suka zauna cikin alfarwansu suna ta gunaguni,
Sun ƙi su saurari Ubangiji.
26Saboda haka ya yi musu kakkausan kashedi,
Cewa shi zai sa su duka su mutu a jejin,
27 # L.Fir 26.33 Zai warwatsa zuriyarsu a cikin arna,
Ya bar su su mutu a baƙuwar ƙasa.
28 # L.Ƙid 25.1-13 Sai jama'ar Allah suka taru suka shiga yi wa Ba'al sujada, a Feyor,
Suka ci hadayun da aka miƙa wa matattun alloli.
29Suka tsokani Ubangiji, ya yi fushi saboda ayyukansu,
Mugawar cuta ta auka musu,
30Amma Finehas ya tashi, ya yanke hukunci a kan laifin,
Aka kuwa kawar da annobar.
31Tun daga lokacin nan ake ta tunawa da shi,
Saboda abin da ya yi.
Za a yi ta tunawa da shi a dukan zamanai masu zuwa.
32 # L.Ƙid 20.2-13 Jama'ar Ubangiji suka sa ya yi fushi.
A maɓuɓɓugan Meriba,
Musa ya shiga uku saboda su.
33Suka sa Musa ya husata ƙwarai,
Har ya faɗi abubuwan da bai kamata ya faɗa ba.
34 # L.Mah 2.1-3; 3.5,6 Suka ƙi su kashe arna,
Yadda Ubangiji ya umarta,
35Amma suka yi aurayya da su,
Suka kwaikwayi halayen arnan.
36Jama'ar Allah suka yi wa gumaka sujada.
Wannan kuwa ya jawo musu hallaka.
37 # 2Sar 17.17 Suka miƙa 'ya'yansu mata da maza hadaya ga allolin arna.
38 # L.Ƙid 35.33 Suka karkashe mutane marasa laifi,
Wato 'ya'yansu mata da maza.
Suka miƙa su hadaya ga gumakan Kan'ana,
Suka ƙazantar da ƙasar saboda kashe-kashenkan da suke yi.
39Ta wurin ayyukansu, suka ƙazantar da kansu,
Suka zama marasa aminci ga Allah.
40 # L.Mah 2.14-18 Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da jama'arsa,
Ransa bai ji daɗinsu ba.
41Sai ya bar su ƙarƙashin ikon arna,
Abokan gābansu suka mallake su.
42Abokan gābansu suka zalunce su,
Suka tilasta su, su yi musu biyayya.
43Sau da yawa Ubangiji yakan ceci jama'arsa,
Amma sun fi so su yi masa tawaye,
Suna ta nutsawa can cikin zunubi.
44Duk da haka Ubangiji ya ji su sa'ad da suka yi kira gare shi,
Ya kula da wahalarsu.
45Saboda su ne ya tuna da alkawarinsa,
Ya sāke ra'ayinsa saboda ƙaunarsa mai yawa.
46Ubangiji ya sa waɗanda suka kama su
Su ji tausayinsu.
47 # 1Tar 16.35,36 Ka cece mu, ya Ubangiji Allahnmu,
Ka komo da mu daga cikin sauran al'umma,
Domin mu yabi sunanka mai tsarki,
Mu kuma yi murna mu yi maka godiya.
48Sai mu yabi Ubangiji, Allah na Isra'ila,
Mu yabe shi yanzu da har abada kuma!
Dukan jama'a za su amsa su ce, “Amin! Amin!”
Ku yabi Ubangiji!

Currently Selected:

Zab 106: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in