Ka tuna da ni sa'ad da za ka taimaki jama'arka, ya Ubangiji!
Ka sa ni cikinsu, sa'ad da za ka cece su.
Ka yardar mini in ga wadatar jama'arka,
In yi tarayya da jama'arka da farin cikinsu,
In yi farin ciki tare da waɗanda suke murna ta fāriya domin su naka ne.