YouVersion Logo
Search Icon

Zab 105

105
Allah da Jama'arsa
(1Tar 16.8-22)
1Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar girmansa,
Ku sanar wa sauran al'umma abubuwan da ya yi!
2Ku raira masa waƙa, ku raira yabo gare shi,
Ku faɗi dukan abubuwa masu banmamaki da ya yi!
3Ku yi murna saboda mu nasa ne,
Ku yi murna dukanku da kuke bauta wa Ubangiji!
4Ku je wurin Ubangiji neman taimako,
Ku tsaya a gabansa koyaushe.
5-6Ya ku zuriyar bawansa Ibrahim,
Ya ku zuriyar zaɓaɓɓensa Yakubu,
Ku tuna da mu'ujizansa masu girma, masu banmamaki,
Ku tuna kuma da hukuntai waɗanda ya yanke.
7Shi Ubangiji, shi ne Allahnmu,
Umarnansa domin dukan duniya ne.
8Zai cika alkawarinsa har abada,
Alkawaransa kuma don dubban zamanai,
9 # Far 12.7; 17.8; Far 26.3 Yarjejeniyar da ya yi da Ibrahim,
Da alkawarin da ya yi wa Ishaku.
10 # Far 28.13 Ubangiji ya yi madawwamin alkawari da Isra'ila,
Ya yi madawwamiyar yarjejeniya da Yakubu sa'ad da ya ce,
11“Zan ba ka ƙasar Kan'ana,
Za ta zama mallakarka.”
12Jama'ar Ubangiji kima ne,
Baƙi ne kuwa a ƙasar.
13Suka yi ta yawo daga ƙasa zuwa ƙasa,
Daga wannan mulki zuwa wancan,
14 # Far 20.3-7 Amma bai yarda kowa ya zalunce su ba,
Ya tsauta wa sarakuna da yawa saboda su.
15Ya ce, “Kada ku taɓi bayina, zaɓaɓɓu,
Kada ku cuci annabawana!”
16 # Far 41.53-57 Sa'ad da Ubangiji ya aukar da yunwa a ƙasarsu,
Ya kuma sa abincinsu duka ya ƙare,
17 # Far 37.28; 45.5 Sai ya aika da Yusufu ya riga su zuwa,
Shi wanda aka sayar da shi kamar bawa.
18 # Far 39.20—40.23 Ƙafafunsa suka yi rauni saboda an ɗaure su da sarƙa,
Aka kuma sa wa wuyansa ƙuƙumi na baƙin ƙarfe,
19Har kafin faɗar da ya yi, ta cika.
Maganar Ubangiji ta tabbatar da gaskiyar abin da ya faɗa.
20 # Far 41.14 Sa'an nan Sarkin Masar ya sake shi,
Mai mulkin dukan sauran al'umma ya 'yantar da shi.
21 # Far 41.39-41 Ya sa shi ya lura da mulkinsa,
Ya sa shi ya yi mulki a bisa dukan ƙasar.
22Ya ba shi cikakken iko bisa dukan ma'aikatan hukuma.
Ya ba shi ikon umartar mashawartansa.
23 # Far 46.6; Far 47.11 Sa'an nan Yakubu ya tafi Masar,
Ya zauna a ƙasar.
24 # Fit 1.7-14 Ubangiji ya sa jama'arsa suka hayayyafa da yawa,
Ya sa su fi ƙarfin maƙiyansu.
25Ya sa Masarawa suka ƙi jinin jama'arsa,
Suka yi wa bayinsa munafunci.
26 # Fit 3.1—4.17 Sai ya aiki bayinsa Musa da Haruna, waɗanda ya zaɓa.
27Suka aikata manya manyan ayyuka na Allah,
Suka kuma yi ayyukan al'ajabi a Masar.
28 # Fit 10.21-23 Ya aika da duhu a bisa ƙasar.
Musa da Haruna ba su tayar wa umarnansa ba.
29 # Fit 7.17-21 Ya mai da ruwan kogunansu su zama jini,
Ya karkashe kifayensu duka.
30 # Fit 8.1-6 Ƙasarsu ta cika da kwaɗi,
Har a fādar sarki.
31 # Fit 8.20-24; Fit 8.16,17 Allah ya ba da umarni, sai ƙudaje da ƙwari
Suka cika dukan ƙasar.
32 # Fit 9.22-25 Ya aiki ƙanƙara da tsawa a bisa ƙasarsu
Maimakon ruwan sama.
33Ya lalatar da 'ya'yan inabinsu da itatuwan ɓaurensu,
Ya kakkarya itatuwansu.
34 # Fit 10.12-15 Ya ba da umarni, sai fāri suka zo,
Dubun dubbai da ba su ƙidayuwa.
35Suka cinye dukan tsire-tsire na ƙasa.
Suka cinye dukan amfanin gonaki.
36 # Fit 12.29 Ya karkashe dukan 'ya'yan fari maza
Na dukan iyalan Masarawa.
37 # Fit 12.33-36 Sa'an nan ya bi da Isra'ilawa, suka fita,
Suka kwashi azurfa da zinariya,
Dukansu kuma ƙarfafa ne lafiyayyu.
38Masarawa suka yi murna da fitarsu,
Gama sun tsoratar da su.
39 # Fit 13.21,22 Ya sa girgije ya yi wa jama'arsa inuwa,
Da dare kuma wuta ta haskaka musu.
40 # Fit 16.2-15 Suka roƙa, sai aka ba su makware,
Ya ba su abinci daga sama da za su ci su ƙoshi.
41 # Fit 17.1-7; L.Ƙid 20.2-13 Ya buɗe dutse, sai ruwa ya bulbulo,
Yana gudu cikin hamada kamar kogi.
42Ya tuna da alkawarinsa mai tsarki
Wanda ya yi wa bawansa Ibrahim.
43Haka kuwa ya bi da jama'arsa, suka fita suna raira waƙa,
Ya bi da zaɓaɓɓun jama'arsa, suna sowa ta farin ciki.
44 # Josh 11.16-23 Ya ba su ƙasar baƙi,
Ya sa su gāje gonakinsu,
45Don jama'arsa su yi biyayya da dokokinsa,
Su kuma kiyaye umarninsa.
Ku yabi Ubangiji!

Currently Selected:

Zab 105: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in