YouVersion Logo
Search Icon

Zab 104

104
Ubangiji yana Kula da Halittarsa
1Ka yabi Ubangiji, ya raina!
Ya Ubangiji Allahna, mai girma ne kai!
Kana saye da ɗaukaka da daraja,
2Ka yi lulluɓi da haske.
Ka shimfiɗa sammai kamar alfarwa.
3Ka gina wurin zamanka a bisa kan ruwan da yake sama.
Gajimare ne karusanka,
A bisa kan fikafikan iska kake tafiya.
4 # Ibr 1.7 Iska ce jakadanka,
Walƙiya kuwa ita ce baiwarka.
5Ka sa duniya ta kahu sosai a bisa harsashin gininta,
Ba kuwa za a iya kawar da ita ba har abada.
6Ka sa teku a bisanta kamar alkyabba,
Ruwan kuwa ya rufe manyan duwatsu.
7Amma sa'ad da ka tsauta wa ruwa,
Sai ya tsere,
Sa'ad da ya ji ka daka tsawa,
Sai ya sheƙa a guje.
8Ya haura kan duwatsu, ya gangara cikin kwaruruka,
Wurin da ka shirya masa.
9Ka ƙayyade masa kan iyaka da ba zai taɓa ƙetarewa ba,
Don kada ya sāke rufe duniya.
10Ka sa maɓuɓɓugai suka gudano cikin kwaruruka,
Ka sa ruwa yana gudu tsakanin tuddai.
11Su ne suke shayar da namomin jeji,
Jakunan jeji kuma, a nan sukan kashe ƙishinsu.
12A itatuwan da suke kusa da wurin,
Tsuntsaye suke yin sheƙunansu suna ta raira waƙa.
13Daga sararin sama kakan aiko da ruwa bisa duwatsu,
Ƙasa kuwa takan cika da albarkunka.
14Kakan sa ciyawa ta yi girma don shanu,
Tsire-tsire kuma don amfanin mutum,
Saboda haka mutum zai iya shuka amfanin gona,
15Don ya yi ruwan inabin da zai sa shi farin ciki,
Ya sami man zaitun wanda zai sa shi fara'a,
Da abincin da zai ba shi ƙarfi.
16Itatuwan al'ul na Lebanon sukan sami isasshen ruwan sama,
Itatuwa ne na Ubangiji kansa, waɗanda shi ya dasa.
17A nan tsuntsaye suke yin sheƙunansu,
A bisa itatuwan fir shamuwa suke yin sheƙa.
18A kan duwatsu masu tsayi awakin jeji suke zama,
Remaye sukan ɓuya a kan tsaunukan bakin teku.
19Ka halicci wata don ƙididdigar lokatai,
Rana kuwa ta san daidai lokacin fāɗuwarta.
20Ka halicci dare, da duhu inda namomin jeji suke fitowa.
21Sagarun zakoki sukan yi ruri sa'ad da suke farauta,
Suna neman abincin da Allah zai ba su.
22Sa'ad da rana ta fito,
Sai su koma su kwanta a kogwanninsu.
23Sa'an nan mutane sukan fita su yi aikinsu,
Su yi ta aiki har maraice ya yi.
24Ya Ubangiji, ka halicci abubuwa masu yawa!
Da hikima ƙwarai ka halicce su!
Duniya cike take da talikanka.
25Ga babbar teku mai fāɗi,
Inda talikai da ba su ƙidayuwa suke zaune,
Manya da ƙanana gaba ɗaya.
26 # Ayu 41.1; Zab 74.14; Ish 27.1 Jiragen ruwa suna tafiya a kansa,
Dodon ruwa wanda ka halitta, a ciki yake wasa.
27Dukansu a gare ka suke dogara,
Don ka ba su abinci sa'ad da suke bukata.
28Ka ba su, sun ci,
Ka tanada musu abinci, sun ƙoshi.
29Sa'ad da ka rabu da su sukan tsorata,
In ka zare numfashin da ka ba su, sai su mutu,
Su koma turɓaya, da ma da ita aka yi su.
30Amma sa'ad da ka hura musu numfashi, sai su rayu,
Kakan sabunta fuskar duniya.
31Da ma darajar Ubangiji ta dawwama har abada!
Da ma Ubangiji ya yi farin ciki da abin da ya halitta!
32Ya dubi duniya, sai ta girgiza,
Ya taɓa duwatsu, sai suka tuɗaɗo da hayaƙi.
33Zan raira waƙa ga Ubangiji dukan raina,
Zan raira yabbai ga Allah muddin raina.
34Da ma ya ji daɗin waƙata,
Saboda yakan sa ni in yi murna.
35Da ma a hallakar da masu zunubi daga duniya,
Da ma mugaye su ƙare ƙaƙaf!
Ka yabi Ubangiji, ya raina!
Ka yabi Ubangiji!

Currently Selected:

Zab 104: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in