Zab 103
103
Yabon Ƙaunar Allah
1Ka yabi Ubangiji, ya raina!
Ka yabi sunansa mai tsarki!
2Ka yabi Ubangiji, ya raina,
Kada ka manta da yawan alherinsa.
3Ya gafarta dukan zunubaina,
Ya kuma warkar da dukan cuce-cucena.
4Ya cece ni daga kabari,
Ya sa mini albarka da ƙauna da jinƙai.
5Ya cika raina da kyawawan abubuwa,
Don in zauna gagau,
Ƙaƙƙarfa kamar gaggafa.
6Ubangiji yakan yi wa waɗanda ake zalunta shari'a ta gaskiya.
Yakan ba su hakkinsu.
7Ya faɗa wa Musa shirye-shiryensa.
Ya yardar wa jama'ar Isra'ila su ga manyan ayyukansa.
8 #
Yak 5.11
Ubangiji mai jinƙai ne, mai ƙauna ne kuma,
Mai jinƙirin fushi ne, cike yake da madawwamiyar ƙauna.
9Ba zai yi ta tsautawa kullum ba,
Ba zai yi ta jin haushi har abada ba.
10Yakan yi mana rangwame sa'ad da yake hukunta mu,
Ko sa'ad da yake sāka mana saboda zunubanmu da laifofinmu.
11Kamar yadda nisan sararin sama yake bisa kan duniya,
Haka kuma girman ƙaunarsa yake ga waɗanda suke tsoronsa.
12Kamar yadda gabas take nesa da yamma,
Haka nan ne ya nisantar da zunubanmu daga gare mu.
13Kamar yadda uba yake yi wa 'ya'yansa alheri,
Haka nan kuwa Ubangiji yake yi wa masu tsoronsa alheri.
14Ubangiji ya san abin da aka yi mu da shi,
Yakan tuna, da ƙura aka yi mu.
15Mutum fa, ransa kamar ciyawa ne,
Yakan yi girma, ya yi yabanya kamar furen jeji.
16Sa'an nan iska ta bi ta kansa, yakan ɓace,
Ba mai ƙara ganinsa.
17Amma ƙaunar Ubangiji ga waɗanda suke girmama shi har abada ce.
Alherinsa kuwa tabbatacce ne har dukan zamanai,
18Ga waɗanda suke riƙe da alkawarinsa da gaskiya,
Waɗanda suke biyayya da umarnansa da aminci.
19Ubangiji ya kafa kursiyinsa a Sama,
Shi yake sarautar duka.
20Ku yabi Ubangiji, ku ƙarfafa, ku manyan mala'iku,
Ku da kuke biyayya da umarnansa,
Kuna kasa kunne ga maganarsa!
21Ku yabi Ubangiji, ku dukan ikokin da suke a Sama,
Ku yabi Ubangiji, ku bayinsa masu aikata abin da yake so!
22Ku yabi Ubangiji, dukanku da kuke halittattunsa,
A duk inda yake mulki!
Ka yabi Ubangiji, ya raina!
Currently Selected:
Zab 103: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979